Connect with us

LABARAI

Sultan Ya Karrama ‘Yan Yi Wa Kasa Hidima 2 A Sakkwato

Published

on


Matasa ‘yan yi wa kasa hidima (NYSC) biyu ne suka samu lambar karramawa da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Muhammadu Sa’ad Abubaka ya ba su, an karrama su ne bisa kwazo da koarinsu na yi wa jama’ar yankin karkara hidima a zamansu na shekara daya da suka yi a jihar Sakkwato.
Shugaban hukumar NYSC na jihar Sakkwato, Mista Philip Enaberue, ne ya shaida wa ‘yan jarida jiya jumma’a a garin Sakkwato.
Ya yaba wa Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar da wannan karrama war da ya yi wa ‘yan yi wa kasar hidimar, yana mai cewa, wannan zai kara karfin gwiwa ga sauran matasan wajen kara kwazo ayyukan da suke gabatar wa a yankunan karkarar jihar.
Enaberue ya kara cewa, wadanda suka amfana da wannan karramawar sun fito daga “2017 Batch A, Stream II” sun kuma yi aiyyukansun na ti wa kasar hidimar ne a yankunan karkarar kananan hukumomin Tangaza da Gada.
Ya kara da cewa, “An samar da kyautar ‘yan yi wa kasa hidima da suka fi sauran hali na gari, an kuma karfafa musu zuwa yankunan karkara don yin aiyyukan daya shafi rayuwar alumma. Ya ce, sakatare na musamman na Sultan, Alhaji Hali Machiddo, ya muka kyautar a madadin Sarkin Musulmin in aka basu tabijin na bango ‘Plasma Telebision’ da aka kiyasata kudinsa ya kai naira 100, 000 ga kowannensu.
Shugaban hukumar NYSC din ya kuma ce, wannan kyauta da karramawar da Sultan ya yi zai yi matukar karfafa ‘yan yiwa kasa hidimar gudanar da aiyyukansu a yankunan karkara maimakon cunkushewa a cikin birane inda jama’a basa amfana da aiyyukan nasu.
Enaberue, ya kuma kara da cewa, an fi bukatar aiyyukan ‘yan bautawa kasa hidima a yankuna karkara fiye da birane. “Muna fatan matasa ‘yan yi wa kasa hudima daga jiharmu ta sakkwato zasu samu kyautar shugaban kasa don kuwa a halin yanzu an fara tantace wadanda za a ba kyautar a taron da zai gudana kwanan nan.”
Ya kuma bayyana cewa, hukumar NYSC ta shiga wata yarjejeniya tare da wasu kungiyoyi masu zaman kansu na hirar da masu yi wa kasa hidima a kan harkoin sana’a sda dogaro da kai a lokacin zamansu na yi wa kasa hidima.
Daga karshe, Enaberue ya ce, ‘Bank of Industry’ da ‘Central Bank of Nigeria’ da ‘Heritage Bank’ da kuma wasu kungiyoyin yaki da fatara sun shiga wwata hadaka na bai wa matasa ‘yan yi wa kasar hudima bashin kudade don karfafa musu ci gaba da sana’o’in dogaro da kai.


Advertisement
Click to comment

labarai