Connect with us

LABARAI

Shirin WASH Ya Fara Zagaye Don Kyautata Sha’anin Ruwa A Bauchi

Published

on


Shirin nan mai yunkurin samar da tsaftataccen ruwa da tsaftar muhalli wato ‘Water Sanitation And Hygiene’ (WASH) a takaice, ya fara rangadi zuwa ga sarakunan gargajiya a jihar Bauchi domin tattaunawa da Sarakunan dangane da muhimmancin nusar da ‘yan siyasa don shigar da muradin samar da ruwa mai tsafta a cikin manufofinsu na neman mukamansu domin kyautata sha’anin.
A lokacin da tawagar WASH wacce ta kunshi kungiyoyin al’umma ciki har da ‘yan jarida suka kai wa Sarkin Ningi ziyara dangane da wannan manufar, tawagar sun shaida wa Sarkin cewar muddin aka nusar da ‘yan siyasa bukatar da ke akwai na su maida hankulansu kan kyautata sha’anin ruwa gabanin da kuma bayan zabensu hakan zai kai ga shawo kan matsalolin amfani da gurbataccen ruwa da al’umma ke yi a fadin jihar ta Bauchi.
Da yake jawabi jami’in da ke kula da shirin WASH a karamar hukumar Ganjuwa Alhaji Mudi Marafa ya shaida wa mai martaba Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya cewar Sarakunan suna da gagarumar rawar da za su iya takawa ta fuskacin jan hankalin masu rike da mukamin siyasa ko masu neman mukaman siyasa kan su bai wa sha’anin kula da ruwa fifiko da shirin samar da tsaftataccen ruwa ga jama’a, kula hadi da tsaftar muhallin wanda a bisa haka ne shirin WASH ke gwagwarmayarsa.
Marafa ya kara da cewa yana da yakinin mukatukar shugabanin suka maida hankalin kan wannan shirin hakan zai rage yawaitar mace-macen kananan yara da yadiwar cututtuka a tsakanin al’umma gami da bunkata tattalin arzikin al’umma; a bisa haka ne ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga masu kada kuri’a da su yi yarjejeniyar da dukkanin dan siyasar da ke son mukaminsa na siyasa kan ya yi musu alkawarin maida hankali kan samar musu da tsaftataccen ruwa da kuma tsaftar muhalli la’akari da zaben 2019 ya sako kai.
Da yake maida jawabi mai martaba Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya ya bayyana muhimmanci wannan shirin musamman in aka yi la’akari yawaitar mace-macen yara kankana da bazuwar cutukka a tsakanin jama’a, a bisa haka ne ya shaida aniyarsa ta mara baya wa shirin dari bisa dari.
A ta bakin Sarkin, “Lallai dukka wakilanmu da suke wakiltarmu a dukkanin fannonin majalisu daga karamar hukumar, majalisar jiha, majalisar tarayya, sanata da gwamnoni idan suka rungumi wadannan ababen da kuka fadi ba shakka rayuwar tamu za ta ci gaba,” in ji Sarkin.
Alhaji Yunusa Danyaya ya bayyana wa tawagar cewar da ya jima yana sanya hanu kan irin wannan shirin da nufin kyautata rayuwar al’umma, a bisa haka ne ya yi alkawarin sanar da ‘yan takara da su sanya shirin samar da ruwa mai tsafta da tsaftar muhallai a cikin manufofinsu ya yakin neman zabe domin cim ma manufar.
Tawagar WASH dai sun fara wannan gangamin ne zuwa ga sarakunan gargajiya domin shawararsu kan su bayar da tasu gudummawar wajen nusar da ‘yan siyasa da kuma masu kada kuri’a kan a bijiro da wannan matsalar a cikin yakin neman zabe da kuma manufofin ‘yan siyasa, shirin ya yi imani idan ‘yan siyasa suka shigar da shirin samar da ruwa mai tsafta a cikin bukatunsu hakan zai kawo gagarumar nasara wajen kare mace-mace a sakamakon shaka ko amfani da ruwa marar tsafta, baya ga nan za a samu habakar tattalin arziki gaya.


Advertisement
Click to comment

labarai