Connect with us

LABARAI

Rasuwar A’ishatu Adamu Ta Girgiza Jama’ar Bauchi

Published

on


Rasuwar Hajiya A’ishatu Adamu matar shahararren Likitan nan a jihar Bauchi wato Dakta Sani Adamu ma’aikaci a babban asibitin kwararru da ke Bauchi, ta grigiza al’ummar jihar Bauchi.
Hajiya Aishatu ta rigamu gidan gaskiya ne tana da shekaru 51 a duniya, ta kuma rasu din ne a shekaran jiya a sakamakon wata gajeruwar rashin lafiya da ta yi fama da shi a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa Teaching Hospital (ATBUTH), da ke Bauchi, tuni dai aka yi mata jana’iza da kaita makwancinta kamar yadda addinin Islama ya shimfida.
Kamar yadda mijinta ke bayyanawa, marigayar ma’aikaciya ce a asibitin (ATBUTH) da ke Bauchi, a lokacin da rashin lafiyar ya sameta tana kan amsar jinya ne a asibitin kwararru da ke Bauchi daga bisani aka sauya mata asibitin jinya a kasar Egypt daga bisani dai ta rasu ne a ATBUTH da ke Bauchi, ya misalta rashinta a matsayin babban rashi a gare shi, ya shaida hakurinta da taimakonta a matsayin abin misali.
Daga cikin wadanda suka kai gaisuwar ta’aziyya da jaje a gidan Dakta Sani Adamu da ke unguwar Fadaman Mada sun hada da tawagar wakilan Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu a karkashin babban limamin Bauchi, Alhaji Bala Ahmad Baban Inna, Sarkin Malaman Bauchi, Alhaji Lawal Baba Ma’aji Abubakar da kuma Ajiyan Bauchi Alh. Bala Ajiya.
Sauran wadanda suka kai gaisuwa domin jajanta wa iyalan marigayiyar sun kunshi shugaban jam’iyyar ACP na jihar Bauchi Hon. Uba Ahmad Nana Garkuwan Ningi, tsohon Sanata Bala Adamu Kariya, Sanata Adamu Ibrahim Gumb, tsohon kwamishinan lafiya kuma dan takarar gwamnan Bauchi Farfesa Sani Malami.
Da sauran fitattun mutane da suka kai gaisuwar jajantawa a bisa rashin mamaciyar.
Da yake gudanar da addu’a na musamman a wajen, Malam Tanko Baba Karami ya misalta Hajiya Aishatu Adamu a matsayin macen da ta kokari wajen kyautata rayuwar jama’a a lokacin da take raye, ya yi addu’ar Allah gafarta mata ya kuma albarkaci bayanta.
Wasu almajiran da suke amsar abinci a wajen marigayin kowace rana, Ahmad Musa da kuma Malam Usman sun bayyana cewar marigayiyar ba ta taba yi musu rowa ko kin ba su abinci ba a duk lokacin da suke isa gareta don neman agaji, sun nuna kaduwarsu kan rashinta da yin addu’ar Allah gafarta mata.
Hajiya A’ishatu Adamu, ta rasu ne ta bar ‘ya’ya shida a duniya, da mijinya Sani Adamu, jikoki da sauran makusanta.


Advertisement
Click to comment

labarai