Connect with us

LABARAI

Masarautar Bauchi Ta Yi Sabon Kakaki

Published

on


Masarautar Bauchi ta ayyana sunan Malam Babangida Hassan Jahun a matsayin sabon jami’in hulda da jama’a na masarautar ta Bauchi.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata kwafin sanarwar daga fadar dauke da sanya hanun mai rikon mukamin Sakataren Masarautar Shehu Jika.
Sanarwar ta kara da cewa daga yanzu Babangida Hassan Jahun shine zai ke magana da yawun Masarautar Yakubun Bauchi.
Sanarwar ta bukaceshi day a yi aiki tukuru domin daukaka darajar masarautar, an kuma horeshi da ya yi aikinsa bisa kwarewa da sanin ya kamata.
Inda nadin nasa ta fara aiki daga ranar 11 ga watan Yulin 2018, tunin kuma ya kasance a ofishinsa a matsayin mai Magana da yawun Masarautar ta Bauchi a halin yanzu.


Advertisement
Click to comment

labarai