Connect with us

LABARAI

Jigawa Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan N2.9 Don Inganta Lafiya Da Ilimi

Published

on


Majalisar zartarwar jihar Jigawa ta amince da kashe tsabar ‎kudi kimanin Naira biliyan uku domin gudanar da wasu ayyuka a fannin lafiya da ilimi.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Bala Ibrahim ne ya bayyana haka a yayin zantawarsa da manema labarai jim-kadan bayan kammala zaman majalisar wadda aka gabatar ranar Larabar makon da ya gabata a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Dutse.
Alhaji Bala Ibrahim ya ce, wannan na daya daga cikin yunkurin gwamnatin jihar na bunkasa fannonin ilimi da lafiya a fadin jihar domin ci gaban al’umma.
Ya ce, cikin wadannan ayyuka akwai, ginin sabbin Asibitoci guda uku a garin Garki da Guri da kuma Buji wadda aikinsu zai lankwame tsabar kudi kimanin Naira bilyan N1.497 kafin kammaluwarsa cikin shekara daya.
Haka kuma ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da kashe zunzurutun kudi har kimanin Naira miliyan N59.56 domin gina makarantar koyon aikin Jinya da unguwarzoma a karamar hukumar Babura da ke jihar.
Ya ce, wannan aikin gina makarantar koyon aikin jinya zai dauki tsawon watanni goma sha biyu kafin kammaluwarsa.
Dangane da fannin ilimi kuwa, kwamishinan ya ce a yayin zaman, majalisar ta amince da kashe tsabar kudi kimanin Naira miliyan N819.60 domin gudanar da ayyukan daban-daban a fannin.
Kwamishinan ya bayyana cewa, wadannan ayyuka sun hada da‎ ginin Ajujuwa uku da Bandaki guda shida-shida a makarantun sakandire 26 da ke sakuna da ‎lungunan jihar baki daya.
Sannan ya kuma ce, ragowar ayyukan sun hada da gyaran makarantu da Ajujuwa da katange wasu makarantu da kuma samar da manyan Injunan ba da wuta a makarantun sakandire biyar a jihar ta Jigawa.
Har wayau ya kuma ce, majalisar ta amince da kwangilar samar da kujerun zama a makarantu har guda dubu 12,243 wanda za a samar da guda dubu 8,243 a makarantun islamiyyu da kuma kimanin guda dubu 4,000 a makarantun Sakandire na boko .
Kwamishinan ya bayyana cewa, majalisar ta kuma amince da samar da gado mai hawa biyu na dalibai ‘yan makarantun kwana kimanin guda dubu 2,000.
Daga karshe ya yi kira ga al’ummar jihar da su marawa yunkurin gwamnatin jihar baya na samar da ayyukan raya kasa domin ci gaban jihar da al’ummarta baki daya.


Advertisement
Click to comment

labarai