Connect with us

LABARAI

Hanyoyin Bi don Kauce Wa Rikici A Zaben Ekiti

Published

on


Muna da bukatar tabbatar da tsaronlafiya da dukiyarkowa a Ekiti. Amma tura ‘yansanda har 30,000 a Ekitin ba shi ne abin da ya dace ba. An dai ta kambama zaben ne kawai. Da yin hakan, ba yadda za a yi mu sami sakamakonzabe na gaskiya.
Muna da matsalolin tsaro ko ta ko’ina, don haka ba ma bukatar ‘yan sanda 30,000 a zaben Ekiti, hakan ya nu nagwamnatin mulki ne kawai a gabanta, amma ba ta damu da jin dadin al’umma ba.
Gwamnatin tarayya ta damu da ta kwace kujerun gwamnaoni ne kawai.
Zabe a Nijeriya magana ne nakudi ko mulki kawai, musamman ma irinkudin da aka sata. To da haka ta ya zamu sami zabe mai inganci?
Abin da yakamata hukumar zabe ta yi domin gujewa rikici ba shi take yi ba. Zabukan da aka yi a baya suke tabbatar mana da hakan, ba za su iya hana a yi magudi a zabe ba. Haka nan tsarin namu ma bai bai wa ita kanta hukumar zabe damar gabatar da zabe na gaskiya ba. Dubi ma maganan karban katin jefa kuri’an, da irin wahalar da mutane suka sha kafinsu samu katin jefa kuri’an.
Idan katura ‘yan sanda 30,000 a wajen zabe, me kake sa ran zai faru? Kasantuwan yanayin zaben, ina ganin akwai bukatar a tura ‘yan sanda wajen, amma ai ba bukatar a ce har 30,000, wanda hakan kusan kashi daya bisa goma na ‘yan sandan kasar nan ke nan? Kwata-kwata Jihar Ekiti ba ta kai kashi daya na ‘yanNijeriya ba, ashe ka ga akwai rashin hankali a kan yin hakan.
Idan kuwa ka yi hakan, ke nan kai da kanka ka kira tashin hankalin ke nan, domin ka tsawwala abubuwa.Tabbas akwai wuraren da a Nijeriyakake da bukatan ka yi hakan, kamar misalign Jihohin Ribas, Bayelsa da dai daukacin Jihohin kudu da ma wasu sassa naJ ihohin Arewa maso gabashin kasar nan, kai har ma da Jihohin midil belt.
Amma ai ba ka da bukaar tura ‘yan sanda 30,000, JiragenHelikwafta biyu, motocin Soji masu sulke 10, motocin ‘yan sanda 250, Jami’an DSS 2000, kawai don za a yi zabe a Jihar Ekiti? Wannan ya nuna tabbas kana kiran da a yi tashin hankalin ke nan.
Sun kuma tura duk wadannan ne ba tare da sun kafa masu sharuddan aiki ba.
Wa zai taka wasu kan su jami’an tsaron burki in su ne suka barke da rigiman? Na san shari’o’ida yawa a kotun koliinda aka sami jami’an tsaron da laifukan sata na akwatunan zabe.


Advertisement
Click to comment

labarai