Connect with us

LABARAI

An Yi Garkuwa Da Matafiya A Hanyar Birnin Gwari

Published

on


A shekaranjiya ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da matafiya da dama a babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Matafiyan wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Legas a cikin babbar mota inda ‘yan bindigar suka tsaida su gami da yin garkuwa da su a daidai wani karamin kauye kusa da Bukuru.
Wani direba mai suna Malam Auwalu wanda ya gane wa idonsa yadda aka yi awon gaba da matafiyan, ya shaida cewar ‘yan bindigan sun harbi tayoyin motar a lokacin da take tsaka da tafiya.
Ya ce, “A lokacin da motar ta tsaya, ‘yan bindigar sun bukaci mutanen da suke cikin motar da sakko daga ciki, inda suka ja su zuwa cikin daji,” In ji shi.
Ya kara da cewa mutane 16 daga cikin fasinjojin sun samu nasarar dawo wa da baya daga cikin dajin amma hakarsu bai kai ga nasara arcewa ba, domin ‘yan bindigar sun sake tasa keyarsu zuwa maboyarsu.
A cewarsa, “Ba zan iya shaida muku hakikanin adadin mutanen da aka yi garkuwa da su din ba domin suna da yawa a cikin motar. Amma sha shida daga cikinsu sun dawo baya sai dai ba su kubuta ba,” A cewarsa.
Direban ya kara da cewa ya ga motaci biyu fake a kan hanyar amma bai da tabbacin ko su ma suna daga cikin wadanda aka yi garkuwan da su.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda ASP Mukhtar Hussaini Aliyu, ya bayyana cewar a ranar Laraba sun samu rahoton yin garkuwa da wasu, inda kuma suka aike da jami’ansu domin ceto wadanda aka sace.
Sai dai ya bayyana cewar ya yi magana da sassan ‘yan sanda na shiyyar amma ba su da wani rahoton an yi garkuwa da wasu mutane a ranar Alhamsi.
Ya shaida cewar jami’ansu na ‘yan sanda sun tashi tsaye wajen hana aukuwar irin wannan aika-aikar.


Advertisement
Click to comment

labarai