Connect with us

LABARAI

Abin Da Ke Hana Jama’a Neman Hakkinsu A kotu

Published

on


Batun tauye hakki da karfa-karfa a matakai daban-daban shi ne al’amarin da kullum ke addabar mai karamin karfi, wannan kuwa ya hada da yadda wasu masu ido da kwalli ko uwa a gindin murhu ke baje kolinsu tare da yin karfa-karfa kan al’amura da yawa wanda ake ganin akwai bukatar tabbatar da adalci a cikinsu.
Sashin Shari’a da jami’an tsaro da kuma mahukunta su ne ke zaman bangon da talaka ke tinkaho da shi, musamman lokacin da ya fuskanaci ana shirin yi masa rashin adalci, ko dai ta fuskar kabilanci ko bambancin addini ko kuma da sunan rashin galihu. A lokuta da dama a kan gamu da irin wannan matsala kiri-kiri a danne hakkin mai karamin karfi, kuma ba yadda zai yi sai dai ya rungumi kaddara, duk da kasancewarsa dan kasa wanda kundin tsarin mulkin kasa ya ba shi damar amfana da kariyar mutunci, da dukiya da rayuwarsa.
Barista Nuhu Shehu Mazadu lauya ne mai rajin wayar da kan jama’a wajen fahimtar ainihin hakkokinsu, a wani shiri da ya saba gudanarwa a wata kafar yada labarai a Kano, ya bayyana cewa ko kadan babu wani dalili da zai sa mutun ya tabbatar da zaluntarsa aka yi ko za a yi, kuma ya zuba ido ba tare da amfana da dokar kasa sashi na 42 sakin layi 1, (a) da (b) cikin baka da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada domin bayar da dama ga duk wani dan kasa wajen bayyana kokensa ta hanyoyi guda biyu, na farko ya bayyanawa a kafar yada labarai cewa an tauye masa hakkinsa iri kaza da kaza, kuma idan aka tabbatar da gaskiyar wannnan korafi za a iya sauke duk wanda ya aikata wannan daga kan mukaminsa kowane ne shi.
Barista Nuhu ya ce dole sai jama’a sun cire tsoro daga zuciyarsu matukar ana maganar neman hakki, daman ana fakewa da tsoronmu ne inda ake yi wa jama’a karfakarfa, ya ce ba tallan sana’armu nake ba, amma yana da kyau kowa ya nemi wani masanin shari’a domin neman shawarsa a duk lokacin da wata matsala ko wani abu da bai fahimci hukuncinsa ba, ko yake ganin ana neman tauye masa hakkinsa.
Saboda haka, shi adalci so ake a tabbatar da shi a kan kowa babu dan bora ko dan mowa, irin wannan rashin adalci ne ya haifar abubuwa masu yawa a cikin lungu da sakunan al’ummarmu, kama daga harkokin Kasuwanci da mu’amillar aikace-aikace da sauransu. Irin haka na faruwa a Kasuwanninmu musamman idan ka shiga Kasuwa irin Kantin Kwari a Kano, inda baki daga kasahen waje ke baje kolinsu yadda suke bukata saboda rashin ingancin bin dokokin kasarmu. Misalai za ka tarar da bakon haure na shigo da kayansa, a dauki ma’aikata ba tare da wata shaidar yarjejeniya ba, sannan ga cin zarafin dan kasa karshen ma bayan ya gama cin moriyarsu ya yi masu korar kare, saboda yana takama da wani hamshakin attajiri mara kishin al’ummarsa wanda ya tsaya masa.
Saboda haka, lallai akwai bukatar jama’a su farka daga dogon barcin da ke neman zame masu ajali, wajen tunkarar duk wani kalubale musamman na bin kadin duk wani hakki da mutum ya tabbatar na sa ne, mu daina razana idan an yi batun tafiya kotu, domin nan ne ma wurin da mutum ya kamata ya garzaya domin a kwato masa duk wani hakki da wani ko wasu suke kokarin yi masa karfa-karfa a kansa


Advertisement
Click to comment

labarai