Connect with us

LABARAI

Zargin Nakasa Gwamna Fayose: Majalisar Wakilai Ta Fusata

Published

on


Majalisar Wakilai Ta Kasa ta nuna rashin jin dadinta da abin da ta ce ya faru na kokarin nakasa Gwamnan Jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose da ake zargin ‘yansanda sun yi yayin wani gangamin jam’iyyar PDP da ya gudana ra nar Larabar nan a jihar
Majalisar ta umurci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umurci rundunar ‘yansandan da sauran jami’an tsaro su nemi gafarar ‘Yan Nijeriya kan abin da ya faru.
Wannan matakin ya biyo bayan amincewa da kudirin da Danmajalisa Yussuf Tajudeen daga Jihar Kogi ya gabatar ne domin daukar matakin gaggawa kan lamarin a zaman majalisar wanda ya gudana a jiya Alhamis. Gangamin da PDP ta shirya gabannin zaben gwamnan jihar da za a yi a gobe Asabar domin tarwatsa taron. A cikin wannan halin ne aka yi zargin cewa ‘yansandan sun far wa Gwamnan wanda ya kai shi ga jin rauni.
Majalisar ta yi tir da faruwan hakan tare da bayyana lamarin a matsayin abin da ya saba wa tsarin mulkin kasar nan.
Majalisar ta bayyana cewa babu wani dantakarar zabe da ke bukatar izinin ‘yansanda ko wata hukuma kafin ya gudanar da yakin neman zabe a mazabarsa a tsakanin lokacin da doka ta shata.
Daga nan sai ta bukaci Hukumar Zabe ta Kasa ta tabbatar da gudanar da zaben na gobe Asabar ya gudana cikin gaskiya da adalci.
Sai dai kuma, da yake tsokaci kan lamarin,
Howeber, Rep. Mohammed Mongonu (APC-Borno) stressed the need to listen to all the parties before making judgments.
He said that all that was abailable to the House were comments in the media, and urged the parliament to inbestigate the matter.
The House, therefore, mandated all relebant committees to inbestigate the remote and immediate causes of the matter.
In his ruling, the Speaker of the house, Mr. Yakubu Dogara, mandated the committee to report back in two weeks for further legislatibe actions.
Wasu dai na ganin Gwamnan shi ma ya wuce gona da iri, domin idan bera yana da sata, daddawa ma tana da wari.


Advertisement
Click to comment

labarai