Connect with us

LABARAI

Yariman Zazzau Ya Ziyarci Gundumarsa Ta Hakimci

Published

on


A cikin satin da ya gabata ne, Alhaji Mannir Jafaru, Yariman Zazzau, ya sami gagarumar tarya daga jama’ar gundumarsa a yayin ziyarar sa ta farko a matsayin Hakimi.
Shi ne sabon Hakimin gundumar Sabon Gari, da ke karkashin Masarautar Zazzau, ta Jihar Kaduna.
Alhaji Mannir Jafaru, Yariman Zazzau, na daya daga cikin Hakiman da suka tsallake gyaran fuskar da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi wa Masarautu a Jihar, tun daga sama har kasa.
A bisa tsarin da gwamnatin Jihar Kadunan ta fitar, Yariman Zazzau shi ya zama cikakken Hakimin Bomo a halin yanzu, hakan ya sa shi fitar da ranar Asabar ta zama ranar da zai ziyarci dukkan dagatan da ke karkashinsa tare da gabatar masu da jawabi a matsayinsa na sabon Hakimi.
Bisa hakan ne, jama’ar kasar Bomo, suka shirya masa gagarumar tarya wanda a tarihi ba a samu kamar sa ba a gundumar.
Wakilinmu ya ziyarci gurin, kuma ya turo mana rahoto a kan lamarin kamar haka;
Tun da sanyin safiyar Lahadi, jama’ar gundumar Bomo da kewaye da suka hada da Dagatai, Alkalai, Malaman Jami’o’i, masu Anguwanni da kungiyoyin kabilu da makarantun Islamiyoyi suka yi dafifi don tariyar sabon Hakimin nasu, Alhaji Mannir Jafaru, bayan tarban sa da suka yi, sun masa rakiya ta musamman zuwa ga gundumomi uku da suka hada da Basawa, Bomo da Samaru.
Sabon Hakimin ya karke ziyarar tasa ne a fadar Sarkin Samaru, Alhaji Dauda, wanda shi ya zama mai masaukin baki, kuma wakilin Dagatan da ke karkashin sabon Hakimin, Yariman Zazzau. A yayin da Sarkin Samaru ya ke jawabin sa a gaban sabon Hakimin, ya fara ne da godewa Allah, da ya ba su shugaba mai adalci, mai tausayi, kuma ya yi godiya da yadda dukkanin kananan Sarakuna da ke karkashin Hakimin suka hada kai suka nuna goyon baya ga sabon Hakimin da aka turo masu, kuma ya yi alwashin za su ci gaba da biyayya da kare martabar Masarautar Zazzau bakidaya. Shima sabon Hakimin, a nasa jawabin ya nuna farin cikinsa tare da godewa Allah a kan yadda ya ga al’umma sun yi dafifi don yi masa tarya, ya ce bai taba zata ba, don haka ya ce, yana fatan zumuncin zai dore kamar yadda ya gani, kuma karshe ya yi kira ga Sarakuna da su zama masu adalci ga jama’ar da suke shugabanta, ya ce hakan shi zai kawo ci gaba da samar da zaman lafiya, kuma ya yi godiya ga dukkan jama’an da suka ba da lokacinsu don su shaida wannan rana.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci wurin akwai, babban Alkali na babbar kotun Abuja (High Court), Mai Shari’a Ishak Bello, akwai kuma Alhaji Abbas Likoro, sai shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Alhaji Muhammad Usman, manya-manyan Limaman Masarautar Zazzau da manyan ‘yan siyasa duk sun halarci wurin.
Bayan kammala taro, wakilinmu ya zanta da babban bako kuma amini ga shi Yariman Zazzau, wato Alhaji Justice Ishak Bello, Kuliyan Zazzau, don jin ta bakin sa game da wannan taro, inda ya ka da baki ya ce, ba abin da za su ce sai godiya ga Allah, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba da irin wannan hadin kai da suka bayar, ya ce hakan zai kawo hadin kai da zaman lafiya, kuma ya taya jama’ar murnar samun Hakimi adali, ya ce da za a samu irin su, Yarima da yawa, da wata matsala ba ta taso ba. Ya yi fatan alheri ga jama’ar da suka nuna masu kara tare da goyon baya a wannan tarya, karshe ya yi fatan Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya, Ya kara wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris CFR lafiya, Ya kuma ba da zaman lafiya ga kasa baki-daya.
Shi ma Yariman Zazzau, Alhaji Mannir Jafaru, a yayin da ya ke zantawa da manema labarai ya nuna jin dadinsa tare da godiya ga Allah, kuma ya yi kira ga daukacin dagatai da masu unguwanni da ya ke wakilta a kasarsa, da su nemi zama lafiya da jama’ar su, ya ce, hakan shi zai bayar da daman samun nasara a duk abin da aka sa gaba, kuma ya yi kira ga matasa da su kaurace wa amfani da miyagun kwayoyi, hakanan kuma ya yi kira ga ‘yan siyasa da su yi siyasa mai tsafta, karshe ya yi fatan iyaye za su sa idanunsu a kan tarbiyyan yara tare da baiwa jami’an tsaro hadin kai don magance shigowan gurbatacciyan tarbiyya a kasa bakidaya, ya yi fatan Allah Ya koma da kowa gidansa lafiya.


Advertisement
Click to comment

labarai