Connect with us

ADON GARI

Yanzu Muka Fara Gwagwarmaya A Kan Yara – Halima Yakasai

Published

on


HAJIYA HALIMA MUSA YAKASAI, babbar jami’a ce a ma’ikatar lafiya ta jihar Kano, gogaggiyar ma’aikaciya a fannin samar da ingantaccen abinci, wacce jajircewarta ta ba ta damar ziyartar kasashe da jahohi masu yawa. Hajiya Halima ta kasance guda cikin masu gudanar da bincike mai zurfi wajen bullo da hanyoyin samar ingantaccen abinci mai gina jiki ga kanana yara. Wakiliyarmu, NA’IMA ABUBAKAR ta yi mana nazari a kan rayuwarta.
Wacece Hajiya Halima Yakasai?
An haifi Hajiya Halima cikin shekara ta 1969 a unguwar Yakasai cikin Birnin Kano. Ta fara karatunta na firamare a ‘Masallaci Primary School’, daga nan kuma ta koma sakandiran ‘yan mata ta shekara, sai kuma
Makarantar ‘yan mata ta Kwa a cikin shekara ta 1981 zuwa 1986. Bayan nan sai ta tafi makarantar koyon aikin jinya da unguwar zumo wadda aka fi sa ni da ‘school of nursing’, daga shekara ta 1987 zuwa 1989 domin samun shaidar karatun kiwon lafiyar al’umma.
Hajiya Halima ta kuma ci gaba da aiki a Asibitoci daban-daban wanda ya hadar da Asibitin Murtala daga nan sai Asibitin yada Kunya daga nan ta koma Asibitin Yara na Hasiya Bayero, daga nan sai Asibitin Yakasai Zumunta daga nan aka mayar da ita Asibitin da ke gidan Gwamnatin Kano, sannan kuma aka sake mayar da ita Yakasai Zumunta. Daga nan kuma aka mayar da ita asibitin Nuhu Bammali, sai aka sake mayar da ita Asibitin Yakasai Zumunta domin wasu matsaloli, daga nan sai Asibitin Abudullahi wase.
Daga nan ne na tafi Sakkwato domin samun karin samun ilimi a fanin jagorancin harkokin lafiya, bayan dawowar ta ne aka mayar da ita Maikatar lafiya ta Jihar Kano a cikin shekara 2011, inda aka ba ta matsayin mataimakiyar Shugaban mai kula da sashin harkokin kula da yara da rainon ciki. Tana kan wannan mukami ne kuma aka ga cancantarta aka ba ta shugabancin sashin lura da ingantattun abinci, mukamin da take kai da shi har zuwa yanzu.

Manyan hidindimunta na rayuwa…
Kasancewarta shugaba a sashin lura da ingantattun abinci da lura da lafiyar yara musamman ‘yan kasa da shekara biyar, Hajiya Halima Yakasai ta kasance guda cikin wadanda ke halartar taruka iri daban-daban da suka shafi batun inganta lafiyar yara da kuma samar da abinci mai gina jiki. kasancewarta jajirtacciyar ma’aikaciyar lafiya ta samun damar bayar da gudunmawa musammman a asibitoci da kuma tarukan kara wa juna sani.

Gwagwarmayarta a bakin aiki….
Kasancewar a duk wani nau’in aiki sai mutun ya kasance jajirttacen mai kishin aikinsa, wannan tasa a cikin zuciyarta ta yi maganar cewa, “Gwargwarmaya kamar yanzu aka fara. musamman ganin halin da yara kan tsinci kansu a ciki da kuma irin shawarar da muke baiwa iyaye mata Musammman wajen shayar da jarirai Nonon Uwa a matakin farko, wannan ke zaman riga kafi ga cututtuka da ke addabar kanana yara”.

Kalubale….
A duk wani tsari na rayuwa dole mutum ya yarda cewa zai gamu da kalubale wanda kuma hakan a lokuta da dama shine ke zaman fitila dake haska nassara a rayuwa. Babbban kalubalen da zan iya fada shi ne wannan aiki namu akwai tafiye-tafiye wanda ke rage mana zumunci a tsakaninmu, sai kuma a wasu lokuta da za ka ga abin da shugaba ke bukata ya saba da ainihin abin da ka’idar abin da aiki ya nuna, kuma dole sai ka bi abin da shugaba ke so, akwai kuma kalubale na fadakar da iyaye mata yadda ya kamata su zabawa yaransu irin tarbiyar da ta dace, musammman abokai ne, makarantu da kuma samar da abinci mai gina jiki domin kauce wa matsalar cutar Tamowa, wadda a halin yanzu tana nan jibge lungu da sako na al’ummma.

Abubuwan da Hajiya Halima ta fi sha’awa a rayuwa…
Gaskiya dai na fi sha’awar Tuwo musamman da miyar kuka, haka kuma ina sha’awar yawan karance-karance musammaman abubuwan addini da na rayuwa sannan kuma nakan so zama da iyalina da maigidana a koda yaushe.


Advertisement
Click to comment

labarai