Connect with us

LABARAI

Yan Bindaga Sun Sace Dan Chana A Karon Farko A Zamfara

Published

on


Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace wani dan kasar Sin ‘Chinese’ mai suna Ren Dajun a tsakar wani daji da ke kauyen Amumu a karamar hukumar Bakura da ke jihar Zamfara.
Ren Dajun dai ma’aikaci ne a cibiyar kasuwanci ta Sinanci da ke kauyen Birnin Tudu a cikin karamar hukumar Bakura.
‘Yan bindigar sun tsaida motar da dan kasar Sin din ke ciki; daga bisani suka yi awun gaba da shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya bayyana cewar tuni suka fara gudanar da bincike domin ceto dan Sin din da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da shi.
Ya kuma shaida cewar sashinsu na musamman masu dakile ‘yan garkuwa da mutane sun baza su domin cetowa gami da kamo ‘yan bindigan da suka sheka wannan aika-aikar.
Daga bisani ya shawarci jama’a da suke taimaka wa rundunarsu da bayanai domin gano masu aikata laifukan ta’addanci a cikin al’umma domin hukuntasu.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa wannan ne karon farko da ake sace wani dan kasar Sin


Advertisement
Click to comment

labarai