Connect with us

WASIKU

‘Ya Kamata Musulmin Nijeriya Mu Hada Kai’

Published

on


Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya. Ina goyon bayan da mu sassauta ra’ayin banbancin akida, mu dena zagin juna da bibiyar juna da sharri, maimakon haka mu hada kai a kan gaskiya ta hanyar yiwa juna uzuri, daga nan ne zamu samu damar magance matsalolin da suke addabar mu.

Saboda na lura makiyanmu suna yakarmu ta bangaren cusa mana kiyayyar juna da banbancin akida, banbancin akida ba zai taba hanawa a fadi gaskiya ba, amma ‘yan hayaniya masu zafin kai su dena tsoma baki cikin addini, a bar malamai da suka amsa sunan malunta su fahimtar da al’ummar musulmi tafarkin gaskiya ba tare da cin zarafi ba.

Abokan zamanmu a Nijeriya sun fimu banbancin akida da dariku masu tsananin zafi cikin addininsu, amma saboda yadda suka hada kai za ka yi tsammanin ba su da wata banbancin akida, da zaran wani abu ya faru suna haduwa su tunkari duk wata matsala da ta taso musu sannan su maganceta ba tare da daukan dogon lokaci ba.

Amma mu yau musulmi abu yana faruwa da wasu jama’ar mu maimakon a kallesu a matsayin musulmi sai a ce ai ‘yan kungiya kaza ne ko kuma akida kaza suke bi don haka mu ba ruwanmu su je can su karata, kuskure ne wannan, ya kamata mu gyara.

Tsarin dokokin Nijeriya idan aka dube shi tun daga farkonsa har karshensa an gina shi ne a kan bayar da kariya da fifiko ga mabiya wasu addinai, tsarin ya zama kishiya ga ‘yancin musulmai da tsarin dokokin musulunci, don haka ina ganin kuskuren wadanda suke cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza wajen shawo kan matsalolin da suke addabar musulmai a Nijeriya ba tare da sun yi la’akari da tsarin dokokin kasar da aka ginashi a kan sharri da zalunci da son-rai da ra’ayi wajen bada fifiko ga wasu mabiya addinai ba, amma idan akwai hadin kan musulmai a Nijeriya babu shakka za a magance dukkan matsalolin.

Matsalolinmu yana a tsakaninmu musulmai, kuma hanyar da za a bi domin shawo kan matsalolinmu shi ne hadin kai kamar yadda Marigayi Malam Albaniy Zariya ya sha nanata fadin haka, lokacin da wasu Malamai a Zariya suka kai karan Malam Albaniy Zariya gaban wani Sarki aka ci mutuncinshi bayan ya fito ya yi jawabi ya ce “da gangan aka hana musulmi su hada kai a Nijeriya saboda ana bada kudi”, miyagun malamai da suke ingiza mu wajen rabuwan kan musulmai ana ba su kudi mu yi kokari wajen gano su sannan mu guje su.

Muna rokon Allah ya hada kanmu a kan gaskiya ya shiryar damu a tafarkin gaskiya ya bamu ikon magance dukkan matsaloli da suke damunmu a Nijeriya.
Sako daga Isma’il Yusuf, Kagarko. 08168499372

Maganar Sabuwar APC
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya. Maganar sabuwar APC ba wani abu ba ne face hakkin ‘yan Nijeriya ne kawai ya fara kama su. Allah ya kawo mana canji mafi alheri.
Sako daga Nasiru Albani, Bauchi.
08167155483

Nazari A Kan Ilmin Boko Na ‘Ya‘Ya Mata
Salam, Editan LEADERSHIP A YAU Juma’a, ina so ka bani dama na bayyana abin da ya ke ci min tuwo a kwarya. Sau da yawa za ka ji ana ta magana a kafafen watsa labarai da wuraren tarurruka cewa mutanen Arewacin kasar nan an bar su a baya musamman a karatun ‘ya`ya mata, ana ta kiraye-kiraye amma shiru kake ji ba wani kwakaran canji, me ya sa?

Wasu mutane suna zargin rashin wayewa da kuma rashin fahimtar riko da al’ adu da addini.
Da farko, masu magana su kan yi tuya su mance da albasa, abin tambaya me ya sanya kiraye-kirayensu ya kasa tasiri a zukatan jama’ar? Me ya sa suke dai-daita jama’ar da wadancan jama’ar da suka rasa wadannan gwala-gwalai (addini da al”ada) da gangan ne masu magana suke mance tasirin addini da al’ada ga al’umma? Addini mizani ne da ke sai-saita kowane bakon abu domin ya a jiye shi a mazaunin da ya dace dashi, rashin irin wannan saitin shi ke kai al’umma ga cigaban mai shiga rijiya.

Idan har aka kasa gyara tsarin makarantunmu ta yadda za su dace da addininmu da al’adunmu, ina ganin zai yi wuya wadannan kiraye-kiraye su iya yin tasiri. Domin duba da irin abin da ke faruwa a manyan makarantun bokonmu, ta kai yanzu yara sun fahimci abin kunya ake gudu watau ciki. Yanzu zamani ya zo da ababen da ke iya hana daukar ciki, wasu iyayen ma haka shi kenan ba a damuwa da irin ta’asar da ake tabkawa a tsangayoyin karatu. Abin mamaki na taba jin ana hira da wani malamin jami’a, aka yi masa tsokaci da matsalar tarbiya da ke faruwa a jami’o’i sai ya kada baki ya ce ai su dama ba an kai masu yara bane su ba su tarbiya a jami’a ba. A takaice wannan dalili ne ya sa wasu iyaye su ke ganin romon da ilmin boko ke badawa bai kai matsayin da zai fanshi addininsu da al’adunsu ba, don haka a kwai bukatar kara nazari.
Sako daga Muhammad Idris, Abuja. 07065279510

‘Yan Arewa Mu Yi Dattara
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a, ina so ku bani dama na fadi damuwata a kan marasa kishin Arewa. Ya kai dan Arewa mai hankali, ya kai dan Arewa mai tunani, ya kai dan Arewa mai ilimi, ya kai dan Arewa mai kishi, ya kai dan Arewa mai son cigaba, ya kai dan Arewa mai son zaman lafiya, ya kai dan Arewa mai son kasarsa, ya kai dan Arewa mai imani, ya kai dan Arewa mutunci. shin yaushe za mu raba kanmu, yaushe za mu fatattaki burgunan kasarmu, yaushe zamu kori karnukan daga masu bakin haushin da suke muna. Rashin kishin kasa da talaka da ke cikin zukatan wadansu ‘yan Arewa ta sa wasu karnuka sun fita daga gidan da ya daga darajarsu zuwa gidan kuraye masu cin naman musai su da iyalansu. Shi ko durwan kare yana ta haushi don shi ma ya samu nashi naman musan ya ci. Ya Allah ka rabamu da hassada da bakin ciki amin.
Sako daga Usman Hamisu, Kaduna. 08160874213


Advertisement
Click to comment

labarai