Connect with us

LABARAI

Ya Kamata Gwamnatin Ta Rushe Kungiyar Dalibai Ta Kasa –Sanata Kani

Published

on


Shugaban daliban jami’ar Bayero da ke Kano, Sanata Muhammad Sanusi Kani ya yi kira ga gwamnatin tarayyar kasar nan da ta rushe kungiyar dalibai ta kasa wato NAN sannan ta kafa sabuwa domin ganin daliban da ke kasar suna amfanar kungiyar.
Sanata Kani ya ba da wannan sanarwar ne a wata hira da ya yi da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja bayan kammala babban zaben kungiyar wanda shugabancin hukumar ya shirya a wannan satin domin zaben sababbin shugabanni.
Kungiyar dalibai ta NAN dai kungiya ce wadda aka kirkire ta domin kula da hakkokin dalibai a fadin kasar nan sannan kuma da kwato wa duk wani dalibi da ke kasar nan hakkinsa a duk inda ake nema a tauye masa.
“ina kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta rushe shugabancin dalibai na kasa sannan kuma ta kafa wani kwamiti wanda zai tabbatar an sakewa kungiyar sabuwar fuska da shugabanci nagari domin amfanin daliban kasar nan” in ji Sanata Kani
Kani ya kara da cewa ‘ Kungiyar dalibai da aka sani da nemowa dalibai hakkunansu da kuma ganin ansamu ci gaba a harkar ilimi a kasar nan ta canja zuwa wani layin daban saboda son zuciya da kuma neman abin duniya”
Sannan ya yi zargin cewa shugabannin zaben sun yi kokarin dage zaben zuwa wata ranar amma kuma wakilai wadanda suka je domin kada kuri’arsu suka yi bore kuma suka ce ba su jiba ba su gani ba kuma ba za a dage zaben ba.
Ya ci gaba da cewa tun farkon zaben an shirya za a yi a ranar biyar ga wannan watan amma saboda anason a shirya wani abu sai da aka kai har ranar 10 ga wata sannan aka gudanar da zaben wanda hakan ya sa wasu daga cikin masu zaben suka tafi ba tare da sun yi ba.
Ya ce yawancin ‘yan takarar da suka nemi a zabe su domin zaman shugabannin kungiyar ba daliba ba ne wasu domin wasu daga cikinsu duk sun gama kuma kawo yanzu babu wani shugaba da za a ce ya ci zabe.
“kawo yanzu babu wani wanda za a ce shi ne shugaba saboda kowa yanzu shugaba ne domin duk wanda ya yi takara a yanzu yana amsa sunan shugaba saboda kungiyar ba ta da inda ta dosa sannan kuma babu wadanda suke tsawatarwa a kungiyar ko kuma daga bangaren gwamnati.
A karshe kuma ya ce yana ganin lokaci ya yi da gwamnati za ta dawo da hankalinta ga wannan kungiya domin kawo gyara da kuma ganin dalibai sun fara jin dadin kungiyar.


Advertisement
Click to comment

labarai