Connect with us

WASANNI

Wasan Karshe: Akwai Aiki A Gaban Mu, Cewar Pogba

Published

on


A dai-dai lokacin da faransawa da dama ke ci gaba da bayyana murnar su bayan nasarar kungiyar kwallon kafar kasar na tsallakawa zuwa mataki ko zagaye na karshe a gasar bayan doke kungiyar kwallon kafar Belgium da ci 1 da 0, akasarin manazarta da wasu daga cikin ‘yan wasan sun bayyana cewa yanzu kam aiki na gaban su.
Dan wasan tsakiya Paul Pogba yan lokuta da kammala wasan, kalaman sa na farko shi ne yanzu aka soma gasar, domin idan aka yi tuni a lokacin gasar cin kofin Turai haka ta faru, Faransa ta tsallaka zuwa mataki na karshe,wanda yan wasan suka kasa lashe kofin.
Pogba ya bukaci karin hadin kan yan wasan kungiyar domin kaucewa sake fadawa cikin wani rudani mai kama da wacan lokaci.
Pogba ya bayyana cewa duk da nasarar da suka yi a karawar su da Belgium, kungiyar kwallon kafar Belgium ba karamar kungiya ba ce kuma ya jinjina musu bias kokari. Da sukayi a wasan na ranar Talata
Kasar Faransa dai zata fafata da kasar Crotia a wasan karshe na gasar cin kofin duniya da akeyi a kasar Rasha a daidai wannan lokaci a ranar Lahadi da misalign karfe hudu agogon Najeriya.


Advertisement
Click to comment

labarai