Connect with us

Madubin Rayuwa

Tushen Lalacewar Tarbiyyar A Cikin Al’umma

Published

on


Masu karatun wannan jarida mai farin jini, Assalamu Alaikum. A makon da ya gabata mun kawo maku shimfida a kan illar rashin bin ka’idojin aure da abin da yake haifarwa. A wannan karon kuma za mu tattauna batun lalacewar tarbiyyar yara da asalin tushen abin don lalubo hanyoyin magancewa.
Lalaccewar tarbiyya tana daya daga cikin illa da dalilan rashin bin umarnin Allah ta wajen bin kaidar zamantakewa
Kamar yadda na fada a baya, uba shi ne jigon Gida shugaba haka Allah ya tsara kuma ya rataya ma shi wannan nauyi na kula da Gida a matsayinshi na shugaba ciyarwa, tufatarwa, ilmantarwa, trabiyarsu, kulawa da hakokin iyalansa ta wajen al’ammuransu me suke ciki, me ke faruwa , me ye akwai, me aka yi daidai me ye ba a yi ba, meye babu ,me ya kamata gwargwadon iyawarsa domin kowa na kasan shi ne don haka Allah ya dora masa nauyi na shugabancin yanzu sau da yawa idan muka duba za mu ga da yawa a wannan lokaci magidanta sukan kasa sauke hakkinsu na maigida shi ne daya daga cikin sillar lalacewar tarbiyyar yara awannan zamanin domin idan muka duba za mu ga duk gidan da ba a samu tsayayyen uba ba, sai a hankali tarbiyyar matar da ta yaran idan ma mata da yawa ne, za ku ga gidan bai da ingantaciyyar zamantakewa, za a fuskanci matsala iri daban-daban
Haka bangaren Uwa ita ma tana taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar tarbiya domin uwaye nagari su ne sillar al’umma tagari.
Babbar rawar da iyaye suke takawa wajen lalacewar tarbiya a yau su ne:
1. Saudayawa tarbiyyar yara takan yi asali ne tun daga iron macen da magidanci ya auro ba tare da nazarin wannan ita ce za ta zama uwar yarana ,ita zan dinga barwa Amana idan na fita ba, ita ce me tarbiyyarsu , wacce idan na fita ba ni da damuwa a gidana na san wacce na bari wanda shi ne babban abin dubawa kuma abu na farko da magidanci ya kamata ya duba yayin neman abokiyar zama domin idan aka sami matsala tun a nan, to idan ba Allah ya kyauta ba farkon illatar rayuwarshi kenan a duniya idan bai sa’a ba har lahirarsa.
2. Halin ko inkula na magidanta ga iyalensu da sakin ragamar komai hannun mace
3. Rashin iya sauke nauyi tawajen ciyarwa, ilmantarwa, tarbiya da tufatarwa.
4. Rashin zama cikin iyalai don fahimtar me suke ciki
5. Rashin shakuwa ko sakewa da iyalin domin kowanne yasake wajen bayyana make faruwa.
6. Kwadayi da son abun duniya na iyaye: ba ku ba yarinyarki abinci ba, wakike ko make tunanin zaibata? Wannan shiyake haifar da sata da bin maza ga yara awasu lokuta kuma iyaye kan nuna halin ko inkula wajen ganin yaransu da sabon abu Wanda basu suka basuba batare da tuhuma ba
7. Gallazawa yara duka, aikin da yafi karfinsu, yawan kyararsu.
8. Matsanancin so, wan a yawancin iyaye a yau ba su son su ga bacin ran yaransu.
9. Rabuwar aure wanda idan aka ci karo da uban ko uwar da ke rikon yaran ba me kulawa bane .
10. Rashin son laifin yara. Domin yanzu sau da yawa idan muka duba za mu ga cewa mafi yawancin iyaye musamman iyaye mata basu son laifin yaransu, sai su yi fada da kowa ko da ‘yan uwansu ne, to wannan yana daya daga cikin lalacewar tarbiyya ta gudun mawar iyaye domin kuwa duk halin da yaronki ke ciki babu mai fada miki.
11. Lalata yaran jama’a. Allah Ubangiji ba ya zalumci, ba zaka lalata dan wani ka yi tunanin naka zai tsira ba.
Da fatan ‘yan’uwana maza da mata za mu kiyaye wadannan abubuwa da na lissafa a sama da kuma karin makamantansu domin gyara zamantakewarmu don Iyalai su ji dadi, makota su ji dadi, uwa uba kuma al’umma baki daya ta amfana saboda zaman tare ya inganta.
Mu hadu a mako mai zuwa idan Allah ya kai mu domin tattauna wani muhimmin batun kuma.


Advertisement
Click to comment

labarai