Connect with us

LABARAI

Majalisar Dinkin Duniya Da Kungiyar Kasashen Afirka Na Shirin Hada Karfi Kan Zaman Lafiya

Published

on


Cikin makon da ya gabata ne, kungiyoyi guda biyu na Majalisar Dinkin Duniya (UN) da takwararta ta, Kungiyar Hada kan Afirika, (AU), suka gudanar da babban taro wanda aka kira shi da taron kara wa juna sani karo na biyu .
Taron wanda aka yi shi a ranar 9 ga watan Yuli, 2018, a karkashin jagorancin babban mai tsare-tsare na kungiyar ta Afirka, Moussa Faki Mahamat, da babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.

Taron dai ya gudana ne a babbar Hedikwatar kungiyar ta Afrikan da ke Birnin Addis Ababa, ta kasar Habasha, wanda ya sami halastan Mutane daga kasashe daban-daban na Duniya.
Wadanda suka zama manyan baki a wurin taron su ne, shugaban tsare-tsaren kungiyar ta Afrika, Moussan Faki Mahamat da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, duk sun gabatar da jawabai a wajen taron, sannan kuma sun nuna matukar farin cikin su game da wannan taron, sun ce za su yi aiki tare tsakanin wadannan kungiyoyi guda biyu, wajen bunkasa ayyukan Gwamnatocin Duniya bakidaya.
Shi dai wannan taron kara wa juna sani kashi na Biyu, ya mayar da hankali ne a kan yadda kungiyoyi biyun za su hada hannu su yi aiki tare wajen samar da zaman lafiya da kuma harkan tsaro a fadin Duniya.
Sun kuma tattauna irin ci gaban da aka samu a taron da ya gabata, sannan kuma sun gabatar da wasu kudurori na ci gaba, wanda ake so ya zama sun kankama a shekarar 2030 da kuma 2063
Kungiyar ta AU da ta UN din kuma sun yi magana a kan yadda za su inganta alakar su wajen samar da hadin kai da gudanarwa wajen nemo hanyoyi dawwamammu na warware matsaloli a kan ka’idan da suka shimfida a tsakanin su.
Ka’idojin dai sun hada da samar da wasu damarmaki da ake samu, da kuma rabon kan iyakan kasashen duniya, da kuma daukar mataki na gaggawa wanda ka iya tasowa a tsakanin kasashe na tashin hankali, da kuma kare kara faruwan hakan a gaba, a kuma sa’ido sosai wajen zaman lafiya tsakanin kasashen Duniya.
Taron ya nuna matukar damuwa a kan yadda kasashe ba sa son bin doka da oda, sannan an nuna matukar damuwa a kan barkewar rigingimu da kuma rashin tsaro a fadin duniya gabadaya.
Don haka suka ce, ya zama wajibi a kara inganta al’adu, ka’idoji, da kuma dokoki a duniya gabadaya.
A nasa jawabin, Sakataren majalisar dinkin duniyar, ya yi kira ne a kan a kara samar da wasu hanyoyi na dubaru wanda za su rinka dakile tashin hankali a cikin duniya, ya kuma ba da shawaran da a kara inganta siyasar duniya, sannan mutane su rinka girmama doka, don da haka ne kawai za a samu dawwamamman ci gaba a duniya.
Ya kara da cewa, ya duba wasu hanyoyi wadanda suke kawo tsaiko ga zaman lafiya da harkokin tsaro a yankin Afrika, an dai duba abubuwan da ke faruwa a kasashe kamar irin Burundi, Afrika ta tsakiya, yankin Kogin Chadi, Kamaru, Congo, Madagascar, Mali da kuma Sudan ta Kudu. An yi ittifaki a kan cewa za a kara ba da goyon baya wajen shawo kan matsalolin da yankunan ke fuskanta, musamman abin da ya shafi tattalin arziki, da kuma kawo abubuwan ci gaba a wadannan kasashen, sannan kuma ya kamata a girmama harkar siyasa a yankunan. Sai kuma batun yankin Sahel da aka tabo wanda sakataren ya ce majalisar dinkin duniya tana goyon bayan matakan da ake dauka, don haka za a kara hada hannu wajen kara inganta matakan.
Hakazalika, Sakataren Majalisar dinkin duniyar, ya yaba ma jami’an tsaron kasashen duniya ne wajen yadda suke sadaukar da kansu wajen kare al’umma, gaskiya sun cancanci a yaba masu.
Shi ma cikin jawabinsa, Shugaban tsare-tsaren kungiyar Afrikan, ya yaba da matakin da majalisar dinkin duniya take dauka a game da rikicin Libiya, ya ce, matakin ya nuna yadda majalisar dinkin duniya take aiki tukuru a kan al’amuran da suka shafi duniya.
Sannan ya yaba ma kungiyar AU din yadda suke aiki ba dare ba rana wajen dakile fitintinu da suke faruwa a Afrika, duk da matsalolin kudi da suke fama da shi, ya ce, a shekarar 2016 sun warware matsaloli kimanin 2320, a 2017 kuma sun warware matsaloli 2378, don haka wannan abin a yaba masu ne.


Advertisement
Click to comment

labarai