Connect with us

LABARAI

Majalisa Ta Shiga Yamutsi Lokacin Da ‘Yan ‘R-APC’ Suka Nuna Kansu

Published

on


Zaman Majalisar Wakilai ta kasa a jiya ya zo da dan wani hatsaniya, a lokuta daban-daban na zaman majalisar, wakilai daga bangaren sabuwar R-APC, sun yi ta kokarin su nu na kansu a duk lokacin da dayansu ya mike domin ya yi magana, inda sauran wakilan da suke cikin ainihin Jam’iyyar ta APC suke nu na rashin amincewarsu da hakan, wanda hakan ne ya yi ta kawo ‘yar karamar hatsaniya a zauren majalisar.
Duk hakan yana faruwa ne a daidai lokacin da wakilan sabuwar R-APC din suke ta kokarin su nu na wa duniya cewa batun rade-radin rabuwar kai da ake yi a tsakaninsu duk zuki tamalle ne. inda suke cewa, duk ma masu karyar wai sun janye daga hadakan da suka kulla da sauran Jam’iyyu, daman can ba su shiga cikin hadakan ba.
Hakanan a jiya din dai, wakilan rusasshiyar Jam’iyyar CPC, daga shiyyar kudancin kasarnan sun shelanta shigan su cikin kawancen na R-APC. Hakanan, wakilinmu ya jiyo karin wasu wakilan Jam’iyyar ta APC da ke ta nu na aniyarsu ta komawa cikin sabuwar bangaren Jam’iyyar na R-APC, yawancin masu nu na aniyar hakan sun fito ne daga Jihohin Kaduna da Kano, wadanda Jihohi ne da rabuwan kan ‘yan jam’iyyar ta APC yake dada bayyana karara.
A yanzun haka, da yawa daga cikin wakilan jam’iyyar ta APC duk sun nannade tutocin Jam’iyyar da ke cikin ofisoshinsu. “Jira kawai kadan ka gani, kafin nan dai da gudanar da zabukan share fagen da jam’iyyu za su yi, nan da ‘yan makwanni kadan,” in ji wata majiya a majalisar da ba ta so mu bayyana sunan ta ba.
Hatsaniyar ta fara tashi ne a Majalisar, sa’ilin da Kakakin Majalisar, Yakubu Dogara, ya bukaci Bode Ayorinde, (Daga Jihar Ondo) da ya mike ya gabatar da mukalarsa kan wani batu da ake tattaunawa a Majalisar. Mikewarsa ke da wuya, sai ya fara gabatar da kansa kamar haka, “Ni ne Bode Ayorinde, wakili a Majalisar nan kuma wakili daga Jam’iyyar R-APC. Nan take sai wani wakilin mai suna Johnson ya mike yana kalubalantarsa, inda yake cewa, su Jam’iyyarsu a hade take ba ta da wani bangare.
Nan fa wakilan majalisar ‘yan Jam’iyyar hamayya ta PDP suka yi ta masu dariya suna zolayarsu gami da yi masu ihun cecekucen da suke yi. Lamarin da sai da ya kai ga sa baki gami da tsawatarwan Kakakin Majalisar Yakubu Dogara. Lamarin ya yi kamar ya lafa, amma a lokacin da Kakakin Majalisar ya baiwa wakilin majalisar Tope Olayanu, daga Jihar Kwara daman yin magana, shi ma da ya mike cewa ya yi, Mai girma Kakakin Majalisa, ni ne Tope Olayanu, kuma dan gani kashenin bangaren R-APC, nan ma sai ‘yan asalin Jam’iyyar ta APC suka sake tasowa da hargowa, wacce sai da aka kwashe sama da dakika 60 ana yin ta. A karshe dai Kakakin Majalisar ya tsawatar da cewa, “Olayanu, ba fa kiranka na yi da ka gabatar mana da kanka ba, ko ka gaya mana Jam’iyyar da ka ke a cikinta. Kiran ka na yi da ka tofa naka albarkacin bakin kadai.” Kusan dai duk a haka zaman majalisar ya yi ta gudana.


Advertisement
Click to comment

labarai