Connect with us

LABARAI

‘Ma Su Sukar Gwamnatin Kaduna Ba Su Cikin Kungiyar ‘Yan Fansho’

Published

on


An bayyana wasu gungun mutane da suke gudanar da taro da suke sukar gwanatin Jihar Kaduna kan fansho a kwalejin Alhuda-Huda da ke birnin Zariya da cewar ba su da alaka da kungiyar ma su karban fansho na Jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar ma su karban fansho a Jihar Kaduna kuma Borokan Zazzau, Alhaji Abdu Ramalan Kwarbai Zariya, ne ya bayyana haka, a lokacin da ya zanta da wakilin LEADERSHIP A YAU JUMA’A a Zariya.
Alhaji Abdu Ramalan ya ci gaba da cewar, a duk mako wadannan gungun mutane da wasu ‘yan korensu, suna gudanar da taro a kwalejin Alhuda-Huda, inda suke bayyana wasu batanci ga gwamnatin Jihar Kaduna, kan yadda su a wajensu babu wani abin kirki da gwamnatin ke yi da ya shafi biyan fansho a Jihar Kaduna.
Ya ci gaba da cewar, dukkanin batutuwan da suke furtawa a wajen wannan taro, batutuwa ne da suke karo da juna, wato, ba su da wani ko wasu hujjoji na bayanan da suke bayyana wa ‘yan korensu.
Zuwa yanzu, a cewar shugaban na masu karban fansho a Jihar Kaduna, Alhaji Abdu Ramalan Kwarbai, kungiyar masu karban fansho a Jihar Kaduna, sun dauki duk matakan da suka dace, domin kare mutuncin masu karban fansho da kuma gwamnatin Jihar Kaduna bakidaya.
Duk da haka, ya nuna matukar damuwarsa na yadda duk wani batanci da ya shafi kungiyar masu karban fansho a Jihar Kaduna daga karamar hukumar Zariya ke tasowa, ya ce, nan gaba kadan ma su wannan hali za su gane abubuwan da suke yi, a kwai kura-kurai ma su yawan gaske, kuma kuskuren da sani ake yinsa.
A dai zantawar da aka yi da shugaban masu karban fansho a Jihar Kaduna, ya yaba wa shugabannin kungiyar na karamar hukumar Zariya, na matakan da suka dauka ga wadanda ke shirya wannan taron batanci ga gwamnatin Jihar Kaduna da kuma kungiyar masu karban fansho da ke Jihar.
Alhaji Abdu Ramalan Kwarbai, ya kara da cewar, abubuwan da wannan gungun mutanen ke yi, bai taba sa a sami wani abu a zuciyarsa ba, ‘’domin duk abin da suke yi, suna yi ne da hukuncin da Allah ya yi’’,sai ya shawarce su da su daina kullin da suke yi.


Advertisement
Click to comment

labarai