Connect with us

Uncategorized

‘Idiomatic Expression’ A Hausance

Published

on


Gabatarwa
Yau zan yi karambanin da na saba yi na shiga gonar da ba tawa ba, wato shiga fagen harshen Ingilishi. Ga masu bibiyar rubuce-rubucen da nake yi a wannan shafi na taba yin Makalar da ta yi biji-biji da harshen Ingilishi ta kai ga har wasu sun kira ni ta waya da nuni da cewa an yi kokari sai dai kanun/taken makalar ya so ya yi zafi.
A yau zan dan dilmiya cikin abin da ake kira Idiomatic edpression/Idioms a cikin harshen Ingilishi. Zan yi ne saboda taimaka wa musamman dalibai na manyan makarantu da na lura a ‘yan kwanakin nan malamansu na Ingilishi na yawan ba su jinga/assignment a kai. Haka su ma ‘yan uwana daliban Hausa, wannan makala za ta taimaka wajen yi musu jagora a wannan fage.
Ma’anar Idiomatic Edpression.
Kamus/Dictionary na Chambers na Elizabeth Mclaren Kirkpatrick bugun shekarar 1980 a shafi na 353, na cewa idiom na nufin zance da ke da ma’anar da ba za a iya gane ta ba, ta daidaikun kalmomin da ke cikin zancen.
Ya ba da misalin his mother passed away. Idan aka dubi jimlar za a ga cewa tana nuni da mahaifiyarsa ta wuce. Ma’anar ita ce Mahaifiyarsa ta mutu, ko kamar yadda masu labaru ke cewa, mahaifiyarsa ta sheka lahira.
Shi kuwa Kamus na Cambridge Adbanced Learner, kashi na biyu, bugun shekarar 2005, na Elizabeth Walter, a ma’anar da ya bayar ta Idiom, cewa ya yi, rukuni ne na kalmomi a tsare da ke da wata takamemiyar ma’ana da ta sha bamban daga ainihin ma’anar kowacce kalma ta kashin kanta. Misali ‘To habe bitten more than you can chew’ na nufin kokarin yin abin da ba za ka iya yi ba.
Shi kuwa Neil Skinner a Kamus dinsa na Turanci zuwa Hausa, da ya wallafa a shekarar 1957 bugun Kamfanin dab’i na Arewa wato Northern Nigeria publishing Company, a shafi na 86 na cewa ‘Idiom’ na nufin hanyar fadin harshe ta karfen salon zance, kari.
Sannan na tambayi wasu malaman Hausa a Jami’a irin su Shuaibu Abdulmumini na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Sashen Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka, fassarar Idiom da Hausa, inda suka ce tana nufin Adon Zance, ko Adon Magana, ko zantuka na hikima.
Wadannan ma’anoni da suka ba ni, suka sa na lalubo littattafan Hausa da suka yi magana akan Adon Zance, da Adon Maganar Hausa, da Zantuka na Hikima da azanci a Hausa.
Sai dai kafin nan bari in kawo wasu misalai da ma’anonin Idiom na Harshen Ingilishi.
1. As meek as a lamb. Yana nufin mutum mai kunya ko shiru-shiru.
2. All hands on deck. Yana nufin kowa da kowa ya taimaka/tallafa.
3. Dead duck. Yana nufin wani mutum ko abu da ake da tabbacin zai mutu ko ya fadi.
4. Adjourn a meeting. Yana nufin dakatar da taro, da ake da niyyar ci gaba da shi nan gaba.
5. A breath of fresh air. Na nufin wani mutum ko abu sabo kuma daban mafi armashi.
6. At stake. Na nufin batu da ake magana akansa.
7. Abobeboard. Na nufin abu a fili babu wata kunbiya-kunbiya ko boye-boye.
8. Air one’s dirty in public. Na nufin bayyanawa jama’a sirrinka da ya kamata ka bar wa cikinka.
9. Blue blood. Na nufin kyakkyawan hali.
10. Bone of contention. Na nufin batun da ake takaddama a kansa.
11. Get the ball rolling/Keep the ball rolling. Na nufin a soma wani abu.
12. In the twinkling of an eye. Na nufin kafin kiftawa da bisimillah/ kan ka ce kwabo.
13. All in one peace. Na nufin lafiya lau ba tare da wata barna ta auku ba.
14. Armed to the teeth. Na nufin rike/mallakar makamai masu tarin yawa.
15. Almighty Dollar. Na nufin bautawa kudi/neman kudi ido rufe, ko bai wa neman kudi muhimmanci fiye da komai a rayuwa.
16. Habe a crush. Na nufin son mutum.
17. A hung jury. Na nufin kasa cimma matsaya bangaren shari’a.
18. Habe two left feet. Matsala a kafa da ta hana mutum takawa.
19. Get the ade. Na nufin hasarar aiki.
20. Tricks of the trade. Na nufin dabara.
Tunda mun kawo guda ashirin da ma’anoninsu a hausance, bari mu koma adon zance, da adon magana da zantukan hikima kamar yadda malamai ke da ra’ayin su ne fassarar idiom.
Adon Maganar Hausa.
Bari mu waiwayi Kamus na Adon Maganar Hausa na Inuwa Dikko da Usman Maccido, da aka fara bugawa a shekarar 1991, da Kamfanin Wallafa Littattafai na Nijeriya Ta Arewa ya wallafa. A gabatarwar littafin, marubutan sun yi bayanin cewa Adon maganar Hausa ya kunshi duk wani tarin kalmomi biyu ko fiye da haka wanda ke haifar da ma’anar da ta bambanta da ta su kalmomin in an kalle su dai-dai da dai-dai, wani lokaci ma har a iske sabuwar ma’anar da ba ta hada kome ba da su kalmomin. Sun ba da misalai kamar haka:
1. A-je-da-muwa. Na nufin bazawara
2. Allura ta tono garma. Na nufin matsala karama ta haifar da babba.
3. Ba hammata iska. Na nufin yin dambe.
4. Baibaya da ruwa a jika. Na nufin bai wa wani kyauta cikin matsi ko a sami taimako daga gare shi, don kuwa ga fitina tafe.
5. |oyon wawa. Na nufin a boye abu amma a bar duk wasu alamun da za su nuna ina aka boye abin.
6. Cali-cali. Na nufin mutum biyu ko fiye da haka su taru su dauki kaya
7. Ci – ma- dauki. Na nufin fitina; naci.
8. Dafa keya. Na nufin ruga da gudu.
9. Daudar duniya. Na nufin kudi ko dukiya.
10. Hawa makahon doki. Na nufin yin kasada.
Ma’anar da su Inuwa Dikko da Usman Maccido suka bayar, ta yi kama da ma’anar Idiom da Kamus na Chambers ya bayar kamar yadda muka gani a sama. Wannan ke tabbatar da fassarar Idiom a matsayin Adon Magana. Yake kuma nuna cewa Hausa ma fa tana da Idiomatic edpression.
Abdulkadir Dangambo a littafinsa Rabe-raben Adabin Hausa sabon tsari, bugun shekarar 2008, wallafar Amana Publishers, a shafi na 69, ya yi bayanin cewa AZANCI wasu maganganun hikima ne guntaye, da akan samu masu kama da karin magana. Abin da ya bambanta su da karin magana, shi ne, su ba su da bari biyu. Zance ne a dunkule wanda yake cike da hikima. Dangambo ya ce wasu sukan kira azanci, salon magana, ko maganganun hikima da sauransu. Dangambo ya ba da misalai kamar haka a shafi na 69:
– Hannun wa ka ci ka tashi
– Fargar jaji
– Gyaran gangar Auzinawa
– Labarin kanzon kurege
– Hannunka mai sanda
– Ihu bayan hari
– Rufin kan uwar dadi
– Fadan goggo a kofa
– Jifar gafiyar |aidu
– Jiran gawon shanu.
Yakubu M. Muhammad a littafinsa na Adabin Hausa bugun shekarar 2005, dab’in madaba’ar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samarun Zariya, a shafi na 37, ya yi bayanin cewa SALON MAGANA wata ‘yar guntuwar magana ce wadda ba habaici ba ce ba kuma karin magana ba. Ya ce Hausawa kan yi amfani da ita ne domin nuna wani yanayi ko hali. Inda Yakubu ya ba da misalai kamar haka:
Kunar bakin wake
Kallon hadarin kaji.
Haka nan a littafin Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Kananan Makarantun Sakandare littafi na daya, na Marigayi Malamina Malam Rabiu Zarruk, da daya Malamin nawa Marigayi Abubakar Kafin Hausa, da Malamina a yanzun haka Malam Bello Alhassan, da aka wallafa a kamfanin dab’i na Jami’ar Ibadan a shekarar 2011, shafi na 53, sun yi bayanin cewa idan aka ce salo ana nufin a yi abu ba kamar yadda kowa ya saba yinsa ba. Suka ce Salon magana yana nufin a sarrafa magana ta fito zakwai-zakwai da kuma gwaninta a furuci da cudanyar sautukan harshe. Sun ba da misali kamar haka:
Tunkuda tunku cikin tukar rukubun tukudin
Tumba yai tubus.

Kammalawa
Kamar yadda na fadi a gabatarwa, wannan makala ta yi karambanin duba Idiomatic edpression na harshen Ingilishi, da ma’ana da misalai, da kwatankwacinsa a harshen Hausa, da ma’anoninsu da misalansu daga wasu littattafai na Hausa, domin taimakawa ‘yan uwana dalibai na Harshe.


Advertisement
Click to comment

labarai