Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Halastattu Da Haramtattun Abubuwa Ga Mahajjaci

Published

on


Daga lokacin da mutum ya yi harama da aikin Hajji, duk wani abu na kayan ado ya haramta gare shi, sai dai abin da ba a rasa ba.
Daga cikin abubuwan da aka halasta ma sa akwai yin wanka idan ya yi dauda, watakila saboda doguwar tafiya ko kuma wanda yake Hajjin Ifradi ne da zai kwashe wasu kwanaki cikin harama ko ga wanda ya samu janaba.
A cikin Muwadda, Imam Malik ya ruwaito daga Nafi’u, daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa shi (Abdullahi bin Umar) ya kasance yana yin wanka kuma har ya wanke kansa alhali yana cikin harama. Abin da ya sa ake tsoron wanke kai shi ne don a kiyaye cire gashi.
Har ila yau, a cikin Muwaddan, Imam Malik ya ce Abdullahi bin Umar ba ya wanke kansa idan ya zo yin wanka bayan ya yi harama har sai idan ya samu janaba.
Imam Malik ya karhanta mutumin da ya yi harama ya game kansa da ruwa (kurmani).
Malamai sun ce ya halasta a yi wanka da sabulu bayan an yi harama domin cire dauda. Kuma ya halasta a goge baki da makilin da sauran su. Wannan ma ya halasta a wurin Hanabilawa da Shafi’awa ba ga Malikawa ba kawai, koda kuwa sabulun yana da kamshi.
Ya halasta mai harama ya rufe fuskarsa saboda warin wani abu ko kura.
Idan mai harama ya rufe kansa da mantuwa ko saboda rashin sani, babu komai a kansa. Sai dai kawai a ce ma sa ya cire. Haka nan wanda ya yanke farcensa da mantuwa ko rashin sani, sai ya yi Istigfari.
Ya halasta ga mai harama ya yi kaho idan ya kamu da rashin lafiya. Zai iya matse kurji ko cire hakori ko yanke wata jijiya a jiki ko wani abu da za a yi wa mai harama a asibiti don ya samu lafiya. Ya tabbata cewa an yi wa Manzon Allah (SAW) kaho a tsakiyar kai alhali ya yi harama da Hajji.
Imamun Nawawi ya ce sun tafi a kan cewa za a iya yi wa mai harama kaho koda kuwa za a yanke gashi a wurin. Yin hakan babu laifi, amma kawai haka mutum ya sa a yi ma sa ba tare da wata bukata ba, wannan laifi ne.
Ya halasta ga mai harama ya yi susa a jikinsa. An tambayi Ummul Mumina Aisha (RA) cewa mai harama zai iya yin susa? Ta ce “eh, zai ma iya kai isa matuka wurin susan jikinsa”.
Babu laifi ga mai harama ya shaki kamshi ko ya kalli madubi. Sai dai Malikawa da Hanafiwa sun karhanta zama a wurin da yake akwai turare mai kamshi.
Haka nan, babu laifi mai harama ya daura jakar kudinsa a jikinsa ko sanya zobe a hannu. An ruwaito wannan daga Abdullahi bin Abbas (RA).
Ya halasta mai harama ya sanya kwalli na magani (idan idonsa yana ciwo), matukar kwallin ba mai hade da turare ba ne.
Babu laifi mai harama ya yi amfani da lema saboda ruwa ko rana ko kuma ya shiga cikin wata rumfa.
Mace za ta iya yin kunshi (lalle) kafin ta yi harama da Hajji, amma ban da bayan yin harama. Domin Malaman Malikawa da Hanafiyawa sun ce yin lalle bai halasta ba a ko wane bangare na jiki bayan an yi harama, walau a wurin mace ko namiji.
Wakazalika, babu laifi mai harama da Hajji ya kashe dabbobi masu cutarwa. Annabi (SAW) ya lissafa wasu dabbobi a matsayin fasikai da za a iya kashewa wadanda suka hada da: Hankaka, Shirwa, Kunama, Bera da Kare Mai Cizo.
Haka nan za a iya kashe maciji, zaki, damisa, kura da sauran abubuwa masu cutarwa. Masu dabbobi za su iya kashe kaska. Shi ma dan fashi za a iya yakarsa.
A takaice dai duk wani abu mai cutarwa za a iya kashe shi, amma idan ba ya cutarwa ko an gan shi kar a taba shi.

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci (1)
An haramta wa mai harama da Hajji ko Umura ya sadu da iyalinsa. Haka nan sauran abubuwan da za su iya janyo saduwar.
Haramun ne aikata duk wani sabon Allah ga mai harama (wannan ma ko babu harama ya haramta ballantana kuma an yi haramar).
An hana wa mai harama da Hajji ko Umura yin jayayya ko gardama ta banza ko rikici da wani. Koda shedan ya zuga wani ya ya tinkaro ka da wadannan abubuwa kar ka biye ma sa, ka yi hakuri.
Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya yi Hajji bai sadu da iyalinsa ba, bai yi batsa ko fasikanci ko sabon Allah ba, zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.” Ma’ana babu zunubi a tare da shi.
Wasu Malamai sun yi sharhin cewa za a iya yin tattaunawa ta ilimi. Amma a wannan zamanin jayayya ta fi yawa, don haka zai fi kyau a yi ta-ka-tsan-tsan wurin yin tattaunawar ma.
Wata rana Shehu Ibrahim Kaulakha ya je Hajji sai ya shiga shagon wani mai sayar da littafai ya sayi littafi ya biya, sai mai shagon ya ce sam ba a biya shi kudin ba. Wanda ya raka Shehu shagon zai bude baki ya yi magana Shehun ya dakatar da shi. Sai ya sake dauko kudin ya baiwa mai shagon.
Sun fito shagon sun kama hanya sai mai shagon nan ya ga kudin, ya biyo su Shehu a guje ya ce ya ga wurin da ya ajiye wancan kudin na farko, sai ya tambayi Shehu cewa, me ya sa tunda ya san ya biya shi bai dage kan haka ba, Shehu ya ce ma sa Allah ya hana jayayya a Aikin Hajji. Don haka a kiyaye sosai.
Haramun ne ga mai harama namiji ya daura duk wani abu dinkakke, sai dai hirami kawai. Amma idan bai samu hirami ba, babu laifi ya daura wando kamar yadda Abdullahi bin Abbas (RA) ya ruwaito daga cikin hudubar da Annabi (SAW) ya yi a ranar Arfa.
Idan mai harama bai samu silafas ba, zai iya sanya takalmi sawu-ciki, amma ya yanke shi zuwa karkashin idon sawunsa kamar yadda ake wa khuffi.
Wannan duk an haramta ne ga namiji. Amma ita mace babu abin da ya haramta mata illa sanya turare, nikabi da safar hannu, kamar yadda Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW).
Haka nan kar ta sanya kayan da aka yi musu rini da turare, amma idan rini ne kawai babu turare shikenan. Bayan wannan, za ta iya sanya duk abin da take so.


Advertisement
Click to comment

labarai