Connect with us

LABARAI

Hajjin Bana: Maniyyata 705 Za Su Sauke Farali A Jigawa

Published

on


A dai dai lokacin da hukumar aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta sanar da ranar 21 ga wannan wata domin fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki, Hukumar aikin hajji da jindadin Alhazai ta jihar Jigawa ta bayyana cewa, zuwa yanzu kimanin maniyyata 705 ne suka kammala biyan kudadensu domin zuwa gudanarda aikin hajjin na bana.
Shugaban hukumar Alhaji Muhammad Sani Alhassan ne ya bayyana haka a yayin da ya jagoranci bada horo na musamman ga ‘yanjaridun da aka zaba domin aikin hajjin na bana wadda aka gudanar a farfajiyar hukumar dake birnin Dutse.
Shugaban ya kuma bada tabbacin cewa, tuni dai hukumar aikin hajjin ta kammala duk wani shirye-shiryen samarda ingantaccen masaukin Maniyyata, abinci da motocin safararsu daga Madina zuwa Makka domin gudanarda ayyukansu cikin kwanciyar hankali.
Alhaji Sani ya ja hankulan ‘yan jaridu musamman wadanda aka zaba domin aikin hajjin na bana da kiyaye doka da dokoki gamida yin amfani da kwarewarsu wajen ggudanarda ayyukansu a yayin aikin hajjin domin tsare mutuncin jihar ta Jigawa dama kasa baki daya.
Haka kuma ya ce, tuni dai hukumar tasu ta samarda ma’ikatan lafiya, tsaro da’yanjaridun da zasu kula da maniyyatan domin tabbatar da yin nasarar samun Hajji mabrur.
Daga karshe ya yi kira ga sauran maniyyata da su baiwa hukumar cikakken goyon baya gamida tsare mutuncinsu da na jihar baki daya a yayin zaman nasu a kasa mai tsarki.


Advertisement
Click to comment

labarai