Connect with us

Madubin Rayuwa

Goron Juma’a

Published

on


Assalamu alaikun. Fatan alkairi ga LEADERSHIP A Yau Juma’a , ina mai farin cikin da wannan fali namu da aka bamu dama domin mu sada zumunci ga ‘yan’uwa da abokan arziki. Allah ya daukaki wannan Jarida mai farin jini a Duniya baki daya. Gaisuwar Joron Juma’a ga Editan wannan Jarida, Abdulrazak Yahuza Jere, sai kuma manyan abokan karatuna kamar su Tasi’u Sirajo (Barrister), da Yunus Abubakar, tare da Rabi’u Abdullahi (baban Tahir), sai kuma Haruna Ibrahim (Baba), da Zakariyya Umar Wade, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Aliyu Muhammad. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Yusuf Shuaibu, Abuja.
08034980391

Gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan Jarida tamu mai tarin albarka. Ina so in mika gaisuwar Goron Juma’a ga abokanaina kamar haka Muhammad Idris, sai kuma Kalifa baba Ahmad, tare da Umar Dogara Inkiya Lauka-lauka,da Adon Wanki wato baban Amir da Muhibbat, Oga Ubale Mai wanki da guga, tare da Zubairu Dogi, daga karshe ina mai mika gaisuwar Goron Juma’a ga Dan ladi Kalmi. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin.
Daga Muhammad Mamman, Kaduna.
07078497517

Bayan dubun gaisuwa mai tarin albarka, tare da fatan Allah ya daukaka wannan gidan jarida ta mu, nake mika gaisuwar Goron Juma’a ga abokan arziki kamar su Salis Kalifa Baba Ahmad, sai kuma babban aminina wato Muhammad wanda aka fi sani da Mamman a cikin garin Kaduna, da kuma Barista Muhammadu Tasi’u Sirajo, da Yunus Abubakar da ke Kaduna, sai Malam Uwaisu Buhari Imam a Abuja, da kuma Muhammad Idris a Lake Biew Homes Phase 2 a Kado, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga mai gidan na Raji Musa Yakubu. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Uwaisu Buhari Imam, Sokoto.
07064756693

Gaisuwa mai dabbun yawa ga ma’aikatan wannan gidan Jaridan da kuma tare da fatan alheri nake mika gaisuwar Goron Juma’a ga Alhaji Bature mai Lemu Ikara, sai kuma Baba Ibrahim Ikara, tare da Zainab Bature Ikara (Ummu Mus’ab) da Babana Mustapha Lawal, daga karshe ina mika gaisuwar Goron Juma’a ga Kwasau Family. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Ahmad Mustapha, Kwasau.
08036681108

Da farko,ina mika sakon gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan fili namu mai tarin albarka. Ina so in mika gaisuwar Goron Juma’a ga masoyana kamar su Alhaji Isa Ibrahim Bida, sai Abba Abdullahi (Baka son tsufa),da Falalu Abdullahi Zaria City, tare da Usman Hamisu Abuja, sai kuma Ibrahim Tukura (Shugaban matasa), da kuma Umar Sani Madaki, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Sulaiman Yusuf mai mata biyu Kadija da Fatima. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Musa Yusuf, Abuja. 08033555442

Assalamu aikum. LEADERSHIP A Yau Juma’a, ina farin cikin da samar mana da dama domin mu sada zumunci ga ‘yan’uwa da abokan arziki. Allah ya kara wa wannan Jaridan tamu farin jinni da daukaka a fadin Duniya baki daya. Da farko, ina mika gaisuwar Goron Juma’a ga mai gida na Alhaji Bello Abubakar, sai kuma matarsa Hajiya Bilkisu Bello Abubakar, tare da ‘ya’yansu Hafiz Bello Abubakar, da Hauwa Bello Abubakar, da kuma Mustapha Bello Abubakar, da Fatima Bello Abubakar. Ina kuma mika sakon gaisuwar Goron Juma’a na musamman ga dangin mamam mu wato Hajiya Bilkisu Bello Abubakar kamar su Hajiya Safiya Ahmad Yabo, sai kuma Hajiya Sa’adatu Ali Haruna, da Hajiya Halimatu Abbas Bella, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Hajiya Hauwa Abbas Bello. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Habibu Bello Abbas, Abuja.
08065718705


Advertisement
Click to comment

labarai