Connect with us

LABARAI

Dan Tsohon Gwamnan Kogi Ya Canza Sheka Zuwa PDP

Published

on


Mohammed Ibrahim Idris, dan tsohon gwamnan Jihar Kogi, Ibrahim Idris, ya fice daga Jam’iyyar APC inda ya koma Jam’iyyar PDP.
A shekarar 2016 ne Mohammed ya bar Jam’iyyar ta PDP ya shiga Jam’iyyar da ke mulki ta APC.
Da yake bayyana wa manema labarai da tururuwan magoya bayansa da suka canza shekan a tare da shi, ranar Laraba a kauyan da aka haife shi na Seke, Mohammed Idris cewa ya yi, ai tun watanni tara da suka shige ne zuciyarsa ta koma Jam’iyyar ta PDP, yanzun dai kawai yana kara tabbatarwa al’umma ne domin su shaida.
Ya kuma ce, ya yanke shawaran barin Jam’iyyar ta APC ce kan imanin da ya yi da cewa Jam’iyyar ta baiwa mutane kunya domin kuwa sam ta gaza a Jihar ta Kogi da ma kasa bakidaya.
Mohammed ya ce, Jam’iyyar ta APC ta gama lalacewa ta yadda ba yadda za a iya gyaranta, ba kuma abin kirkin da za ta iya tsinana wa al’umman kasannan da suka zabe ta.
Daganan sai ya sha alwashin yin aiki tukuru tare da shugabannin Jam’iyyar ta PDP domin ganin ta dawo kan mulkin kasarnan a shekarar 2019.


Advertisement
Click to comment

labarai