Connect with us

ZAMANTAKEWA

Daga Littafin Amanna (8)

Published

on


Bai san dokokin da ake bi ba kafin a shiga ciki amma ya tsaya a baya yana kallon yadda masana ke yi, biyan kudi ake kafin a shiga kudi mai yawa kuwa dan haka sai ya juya ya tafi bakin get in da ya hango injin fitar da kudi ATM ya ciro kudi da yawa ya zuba a aljihu, ya dawo ya biya ya shiga. Ya tsinci kansa a cikin wata irin kuntatacciyar rayuwa, idanuwansa suka dinga hasko masa abinda bai shirya gani ba, kunnuwansa suka dinga jiyo masa abinda bai halatta ba. Babu abinda ya ke tashi a wajen sai kida ana ta casu, kan kace kwabo ‘yan mata sun baibaye shi haka yake warbar da su yana tunkude su har suka gaji da binsa suka kyale shi, ya ci gaba da zagaye yana neman abinda ya ke tunani ya gani. Yana ta ci gaba da zagayawa har ya gama zagaye ‘yan rawar nan tsaf bai ga idon sani ba, ya dawo ya zagaye wadanda ke zazzauna suna kora ruwan hajijiya nan ma bai ga kowa ba, har ya juya zai fita sai ya jiyo wata murya wacce ta yi masa kama da muryar da ya sani kuma cikin yarensa ake yin magana wato Hausa. Ya juya da sauri ya dubi in da maganar ke fitowa sai yayi arangama da yayan Nauwara matarsa, Na’if uwarsu daya ubansu daya Nauwara amaryarsa shi da Laurat. Laurat kawar Nauwara ce sosai kuma makwabciyarsu ga gida ga gida kamar yadda ya ke da Khamis, sun yi rawa sun gaji sun sha abar sun yi tatul suna tangadi.
“Subhanallah” Iziddin ya fada a bayyane, yayin da ja baya ya tsaya a gefe yana kallonsu kallo na takaici. Bai yi mamakin Na’if ba saboda ya san halinsa daman iyayen suna ta fama dashi bayan sata da shaye-shaye har da neman mata, yana daya daga cikin masu saka Na’if a gaba ayi masa fada ya daina wannan halin. Amma yayi mamakin Laurat sosai, bai taba zaton itama haka take ba dan haka ya zama dole ya raba matarsa da wannan muguwar kawa. Su ka hada ido da shi amma basu gane shi ba saboda ya canja kama, ya ji dadi da yin hakan.
Ya ci gaba da waiwaye-waiwaye sai ya yi kicibus da Aljannah ta tunkaro shi gadan-gadan sai ya shide a tsaye ya zaci ta gane shi, da ta zo daf da shi sai ta kauce ta shige ashe ba wajensa ta zo ba, ta nufi wajen sayar da lemo da giya ta sayo lemon da aka aiko ta, ta dawo ta wuce ta gabansa tana tafiya kamar silan kara wai nan riga da wando ta saka (jeans da t-shirt) kanta babu dankwali ta saka ribbon ta tufke gashin kanta, da yake tana da gashi sosai. Iziddin na biye da ita a baya lungu-lungu sako-sako har ta isa wani katafaren falo mai dauke da jajajen kujeru da jan kafet na alfarma, sun fi seti goma an zagaye, mata da maza suna zazzaune ana ta masha’a nan ne fadar manyan ‘yan iskan. Kirjinsa ya ci gaba da dukan uku-uku, lallai yau ya ga tashin hankalin da bai taba ganin irinsa ba, Zahida da Khamis ya hango tare suna zazzaune suna ciye-ciye da shaye-shaye suna dariya suna shewa yayin da idanuwan Iziddin suka cika da hawaye ya laluba wata kujera da ke gefe ya zauna. Ya daga kai ya sake kallon Zahidah shigar da ta yi bai taba ganin irinta a ido biyu ba sai dai a fim din turawa, matsatstsiyar riga ce ja iya cinya, babu hannu a rigar sai dogon takalmi mai tsinin gaske launin ja. Kanta babu dankwali ta zubo kitson da aka yi mata na karin (attachment) har gadon bayanta, kasancewarta fara ce sosai sai ka rantse nasara ce, jikin nan sanbal jajawur, gefenta kuwa Khamis ne abokinsa shima shigar ta tantiran ‘yan duniya riga ce ya saka bata da hannu da wando iya guiwa, yana kora wani abu a kofi bai tantance ba lemo ne ko giya.
Aljannah kuwa da ta kai lemon sai ta rabe a gefe ta tsaya, yayin da wani tantirin dan iska ya zagayo ta bayanta ya yi mata cakulkuli ya daga ta sama cimak yana shilla ta kamar wata mage. Ta calla kara gaba daya aka waiwayo ana kallonta, sannan aka dinga sheka dariya ana kyakyatawa irin ta zamanin jahiliya.
Zahidah ta yi dariya ta ce “Liyo ka ajiye min ‘yata bata saba ba, ka barta ta girma tukunna


Advertisement
Click to comment

labarai