Connect with us

RA'AYINMU

Batun Kawo Karshen Zubar Da Jini A Manyan Hanyoyinmu

Published

on


Fashewar tankar mai inda kuma nan take ta kama da wuta na kwana-kwanan nan a wajen gadar Otedola da ke kan babban titin Legas zuwa Ibadan, wanda akalla mutane 12 suka mutu a wajen nan take, sa’ilin da motoci 54 suka kone kurmus, ya sake farfado da bukatar yin wani abu cikin gaggawa ga gwamnatinmu ta yadda za ta kawo karshen ire-iren wadannan hadurran da a kullum suke ta faruwa bisa manyan hanyoyin namu. Jim kadan da faruwar hadarin, sai gwamnatin Jihar ta Legas ta fitar da sakamakon binciken farko na dalilin faruwar hadarin, wanda ta ce binciken ya nu na cewa, matsalar ita kanta motar da kuma yanayin cinkoson motocin da ke bisa hanyar ne a lokacin gami da kasawan da direban motar ya yi na iya sarrafa motar ne ya janyo aukuwar hadarin. Wanda duk hakan da an iya kiyaye faruwarsa, idan da a ce gwamnati tun farko ta yi abin da ya kamata.
Cikin wani yunkurin hana sake aukuwan hakan na gaggawa, gwamnatin sai ta hanzarta fitar da wata sanarwa wacce a ciki take sanar da hanyoyin da ya kamata manyan motocin su rika bi. Kwamishinan Zirga-Zirga, Mista Ladi Lawanson, nan take ya sanar da duk masu ruwa da tsaki a kan zirga-zirgan manyan motocin da suka hada da, kungiyoyin, ma’aikatan mai da iskar gas, (Nigeria Union of Petroleum and Natural Gas Workers), kungyar masu manyan motoci da ke tashar ta Jiragen ruwa, (Association of Maritime Truck Owners), kungiyar masu tuka manyan motocin dakon man fetur, (Petroleum Tanker Dribers), kungiyar masu motocin zirga-zirga da masu manyan motocin dakon manyan kaya ta kasa, (National Association of Transport Operators and Container Truck Owners Association of Nigeria) da dai makamantansu, inda Kwamishinan ya sanar da su cewa, gwamnati ta ba su wa’adin kwanaki 30 da su dauki matakin tabbatar da motocin nasu sun cancanci tafiya a kan hanyoyin namu ta hanyar samun takardar shedar da ke tabbatar da hakan.
Abin takaici ne cewa, gwamnatin ba ta farkawa daga barcinta har sai irin wannan mummunan lamarin ya auku. Hadarin da ya auku na kan gadar ta Otedola, da ire-irensa a ‘yan kwanakin nan, ya nu na cewa, gwamnati ta gaza wajen tilasta yin aiki da dokokin hanyoyin nata. Idan har da a ce gwamnatin tana yin abin da ya dace wajen tabbatar da ana bin dokokin hanyar, da tabbas duk abin takaicin da muke ta gani yana faruwa a yanzun na hadurran motocin dakon man da ma masu daukan manyan kayan da sukan fado su kuma turmushe wasu kananan motocin duk bai faru ba, ko kuma akalla da an sami nasarar rage shi matuka gaya.
A shekarar da ta gabata, wani babban jami’in hukumar kula da hanyoyin namu, (FRSC), Mista Boboye Oyeyemi, ya bayyana cewa, sama da mutane 1000 ne suka mutu a tsakanin watan Disamba 2016 zuwa watan Janairu 2017, a sanadiyyar hadurran manyan motocin dakon man. Abin bakin ciki ne ganin cewa, yawancin manyan motocin da ke jigila bisa hanyoyin namu sam ba su cancanci tafiya a hanyoyin namu ba, kwararrababbu, tayoyin mafiya yawansu duk sun sude wasunsu ma tayoyin a mace suke, amma hukumomin gwamnati da aka dorawa alhakin kare lafiyar hanyoyin namu daga iren wadannan motocin da ba su cancanci bin hanyoyin namu ba, sam ba sa yin aikin nasu yadda ya kamata. Idan aka kula ma da ire-iren wadannan motocin, da yawansu ma ko fitullun baya ma ba su da su, ba siginoni, cikakkun fitullunsu ma na gaba duk sai a hankali, fitullun nu na alamomin gargadi hatta ma lambobin kirki ma ba su da su. Kai duk wata ka’ida ta tuki ma sun saba mata, da suka hada da, sanya na’urorin nu na gudun mota, da lura da yadda aka shirya ma lodi a bisa motocin. Yawancin kuma manyan motocin dakon mai ba su da birkin kirki, in ma akwai shi din, amma dai ga su nan an kyale su suna ta shirga gudu a kan hanya. Kai babban abin takaicin ma shi ne, yawancin direbobin irin wadannan motocin za ka taras duk a buge suke ko kuma akwai barci a idonsu sa’ilin da suke tuka motocin. Sam ba sa damuwa da lokacin wuce wasu motocin da ke kan hanyar a hawa ne ko a kwana, wanda hakan kan tilasta wa masu ababen hawa sauka daga kan titunan gudun kar su danne su. Hakanan kuma bincike ya nu na, yawancin direbobin manyan motocin ma ba su kware da iya sarrafa manyan motocin ba. Duk da kasantuwan muna da hukumomi daban-daban masu kula da zirga-zirgan, ga su BIO nan, ga FRSC, ga sashen ‘yan sanda masu kula da ababen hawa, da hukumar da aka dorawa alhakin tabbatar da lafiyar masu bin hanyoyin.
Amma duk ga alama ba sa aikin nasu yadda ya kamata, domin a lokuta da yawa ma ana tuhumarsu da karban na goro ne daga direbobin, domin su kawar da ganin su kan lafiyar motocin. Akwai kuma rahotannin da ke nu ni da yadda wasu masu fada aji kan zama gagarabadau wajen take dokokin hanyan, musamman kasantuwan yawancin wadannan manyan motocin daga na dakon man har na dakon kaya, yawancinsu wasu masu kumbar susa ne ke mallakinsu. Kan haka, ya zama tilas ga hukumomi kama daga na Jihohi har zuwa na tarayya da su nu na doka a matsayin ba sani, ba sabo. Matukar dai ana son tsarkake hanyoyin namu, a kuma kaucewa shigen hadarin da ya faru a kan gadar ta Otedola, ya zama tilas a dauki halin ba sani, ba sabo wajen yin aiki da dokokin hanyoyin namu. Musamman ga direbobi da kuma iyayen gidansu masu mallakan motocin.
Muna kira ga gwamnati da ta dauki matakan da za su tilasta wa masu aiki a wannan sashe na sufurin yin abin duk da ya dace ko kuma su fuskanci fushin hukuma. Hukumar kiyaye hadurra ta FRSC, kamata ya yi ta dukufa wajen yin aikinta sosai ta yadda za su hana duk wata babbar motar da ba ta cancanci tafiya a kan hanya ba kaucewa daga hanyoyin namu. Ya kuma kamata gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su hada kai da hukumar albarkatun na man fetur, DPR, wajen kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyin da ake yi a kan manyan hanyoyin namu. Duk babbar motar da ba ta cancanta ba, sam bai kamata a kyale ta a bisa hanya ba, ballantana ma har a barta shiga tahsoshin Jiragen ruwan namu domin dauko kayan da zai iya kamawa da wuta da zaran ya ji kyas, wanda hakan jefa rayukan al’ummanmu ne a cikin hadari.


Advertisement
Click to comment

labarai