Connect with us

WASANNI

Barcelona Tana Takara Da Madrid Kan Hazard

Published

on


Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tabi sahun abokiyar hamayyarta ta Real Madrid wajen neman dan wasan Chelsea, Edin Hazard wanda zai kai kusan fam miliyan 100.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce dai ake ganin zata siyi dan wasan mai shekaru 27 a duniya domin maye gurbin Ronaldo wanda yakoma Jubentus a wannan satin.
A kwanakin baya dai dan wasa Hazard ya bayyana cewa idan har kungiyar bata siyo manyan ‘yan wasa ba zai iya barin kungiyar sannan kuma ya ce yana jira yaga wanda zai zama mai koyar da ‘yan wasan kungiyar a kakar wasa mai zuwa.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dai tana shirin siyan dan wasanne bayan ta dakatar da neman da takewa dan wasan Tottenham, Erickson wanda take ganin zai maye mata gurbin Andre Iniesta wanda yayi ritaya daga kungiyar.
Hazard dai yanzu yana kasar Rasha inda yake wakiltar kasar sa ta Belgium a wasan neman na uku na gasar cin kofin duniya inda zasu fafata da kasar Ingila bayan sunsha kashi a hannun kasar Faransa daci 1-0 yayinda kasar Ingila kuma tayi rashin nasara a hannun kasar Crotia daci 2-1.


Advertisement
Click to comment

labarai