Connect with us

Madubin Rayuwa

Ana Zaton Wuta A Makera…

Published

on


Wata rana a unguwar Gani-butsu da ke tsakiyar Kasar Najarana, ya faru cewa wasu barayi sun faki numfashi sun je gidan wani Alhaji sun kafta musu sata ta yankan-kauna. Domin kuwa, ba ya ga tsabar kudade da suka kwasa,hatta kayan sawa irin riguna da wanduna da takalma da atamfofi da mayafai da sarkoki ba su tsira ba daga wadannan barayi.
Ashe cikin wadannan barayi akwai shugaban ‘yan sintiri na unguwar ta Gani-Butsu, amma da yake fuskarsu na rufe ne da wasu bakaken yankuna, hakan sai ya sanya babu wanda zai iya shaida shi. Sai dai wani abu da Dansintirin bai sani ba shi ne, yayin da ya tasa keyar Suwaiba zuwa dakinta don karbar sarkokinta, bayan ya kwaso, wajen fitowa daga dakin, sai wata kusa da aka kafe dab da bakin kofa ta dan fizgi hankicin fuskarsa, duk da rabin fuskar tasa ta fito, amma nan da nan ya mai da tsummar fuskarsa.
Na’am, Suwaiba ba ta gama gane fuskar dansintiri ba, amma dai kam ta shiga kogin wasu-wasin, shin, anya wannan barawo ba Tanimu ba ne shugaban ‘yansintiri? Amma nan da nan wata zuciyar ta ankarar da ita cewa, idan fa mutum bai iya kama barawo ba, to fa barawon zai kama shi. Saboda haka sai ta yi wurgi da wannan tunani. Nan dai zugar wadannan barayi suka gama yashe gidan Alhaji Hashimu, su ka yi musu karkaf. Wani abu da ya kara dugunzuma ran Suwaiba shi ne, har barayin za su fita bayan wawashe komai a gidan, sai wannan da take yi wa kallon dansintiri ya umarci wasu katti biyu da su shiga dakin girki su duba su gani ko akwai wata mamora? Bayan sun shiga sun fito, sai suka ce da shi;
“Maigida, babu komai sai kayan abinci”
Sai ya ce da su;
“Dan ubanku! Tun da kayan abincin ba Alkur’anai ba ne ai sai ku kwaso su. Sannan, ba wai danyen kayan abinci kawai za ku kwaso ba, har ma da dafaffe, ko da kuwa Indomi ce”
Jin wannan umarni ne ya sanya, hatta gishiri da ashana wadannan barayi ba su daga wa kafa ba, sai da sukai awon-gaba da duk wani abin-amfani. Abin da kuma suka san cewa yana da amfani amma fita da shi bai da ma’ana, sai su lalata shi nan take, kamar ruwan dumi. Don kuwa, wasu manyan-manyan fulas biyu da suke cike da ruwan shayi, sai da yaran Tanimu Dansintiri suka bude su suka kyalayar ta ruwan ciki.
Salon irin wannan sata ta yankan-kauna da aka yi a gidan Alhaji Hashimu, tai matukar daure wa al’umar unguwa kai washegari da labari ya bazu. Abu na biyu mafi haushin ma shi ne, Alhaji Hashimu ya kasance Attajiri ne nagari, wanda yake dare da rana cikin taimakon jama’a yake, amma a wayigari an yi masa irin wannan diban-albarka haka? An yi masa sata, an firgita iyalansa haka siddan ba da hakkinsu ba.
A saukin kai da kawaici irin na Alhaji, duk wanda ya zo yi masa jaje, sai a ji yana cewa, shi fa ya bar wa Allah, Shi ne kadai wanda zai bi masa hakkinsa Duniya da Lahira. Wani abu da ya fara fusata mazauna wannan unguwa ta Gani-Butsu shi ne, shin wai, Kungiyar ‘yan sintirin unguwa suna mene aka tafka irin wannan uwar sata haka a gidan Alhajin? Alhali shi ne mutumin da ya fi kowa tallafar kungiyar da lokacinsa da aljihunsa a kaf cikin unguwar. Saboda haka ne ma jama’a ke gunagunin cewa, in dai har ya zamana ‘yansintiri sun yi shakulatin-bangaro da kare mutuncin gidan Alhaji, to kaf din unguwar waye zai sha? Waye kuma zai saki jiki nan gaba a unguwar har ya iya barci da idanu biyu? Wannan tuntuni sai ya bayu zuwa ga neman tilasa Alhaji da ya dau mataki game da irin wannan cin-kashi da ya riske shi har gida.
Hakika Alhaji Tanimu bai da niyyar daukar wani mataki game da wannan lamari, amma wasa-wasa bayan kwanaki biyu da afkuwar abin, labari ya iske D.P.O. na yankin har ofishinsa. DPO’n bai yi wata-wata ba ya gaiyaci Alhaji da iyalansa zuwa can ofishin nasa.
Baya ga jin ta-bakin Alhajin da kuma iyalansa, sai DPO ya tambaya ko unguwar na da Kungiyar ‘yansintiri masu kewaya unguwar da dare? Bayan amsa masa da “Eh”, ne, sai ya nemi da a kira masa Shugaban Kungiyar. Amma ko da aka aike gida a kira shi, sai Matarsa ta ce a fada wa DPO cewa tun Shekaranjiya da dare ne Iskokai suka shafe shi. Haka ne Tanimu ya tsar awa Maidakin nasa ta fada. Bayan an fadi wa DPO abin da Matar Tanimun ta ce, nan da nan sai Suwaiba Matar Alhaji ta dan zakuda daura da DPOn ta yi masa wani kuskus. Sai aka ga DPO ya ce a je a ce wa Matar Tanimu su taho da Maigidan nata, yanzu za su koma.
Bayan kamar rabin sa’a, sai Dan aiken ya dawo ya fadi ma DPO cewa, wai yanzu a na yi wa Dansintirin “rukiyya” ne, shi ya sanya ba zai sami damar zuwa ba. Daga nan, sai aka ga DPO ya bai wa wasu kattin yaransa hudu umarnin su je su taho da Tanimun, da ma mai yi masa rukiyyar.
Ashe yayinda Suwaiba tai wa DPO rada a kunne, ta labarta masa ‘yar shakkar da take yi ne game da wanda kusa ta yage wa kyallen fuskarsa, wanda ke dan yin kama da Dansintirin. Daga nan ne DPO ya dan fara gano ‘yar burum-burum din da dan sintirin ke son yi.
Saboda kwarewa, bayan dan aiken DPO ya koma a karo na biyu, sai Tanimu ya kira wani abokin burminsa na harkar kuruciyar bera da suke yi, ya zama tamkar shi ne mai yi masa rukiyyar. Ashe ita ma matar Tanimu, sarai ta sani maigidan nata mai dauke-dauke ne, amma saboda duniya da take kamfata da tsinke a gidan, sai ta wayigari kwarya na bin kwarya.
Bayan an kwashi dansintiri da mai rukiyya zuwa ofishin ‘yan sandan, sai matarsa ta rarumi mayafinta tai yo waje, ta biyo sawunsu a mashin din ‘a daidaita sahu’. Ko da suka isa Ofis, sai DPOn ya ce da mai rukiyyar, ya ba shi minti 15 ya dawo da Tanimu cikin hayyacinsa.
Nan dai malamin bogen yai ta jaye-jayensa na karya, shi ko gogan naka Tanimu sai wasu sambatun iska ne ya ke yi. Wani abu da ya daga wa Tanimu hankali shi ne, ya ga sadda Suwaiba ke cewa DPO Wallahi wandon ne a jikinsa. Ya ga ta nunawa DPO wandon dake sanye a jikinsa. Nan fa zuciyarsa ta ba da wani rassss!!!! Ya fara tunanin cewa akwai yiwuwar asirinsa ya tonu ne.
Hakika Tanimu ya tabbatar da cewa, da wancan wandon sanye a jikinsa ne suka je sata gidan Alhaji Hashimu. Amma sai yai wani kokarin nuna wata kwarewa, ai tun da rukiyya ce ake masa, saboda haka duk abin da ya furta ba shi ne ya fada ba, Aljani ne ya fadi. Kuma idan aka yarda yana da Aljan, dole ne a rika yi masa uzurin cewa, yawancin abubuwan da yake aikatawa munana, ba yin kansa ba ne, yin Aljanun ne.
Idan mai rukiyyar ya tsala masa bulala, sai a ji shi yana ta wasu surutai iri-iri. Ga wasu daga soki-burutsun;
“…Ai gobe ma za mu je gidan Shugaban Kasa da Gidan Gwamna mu yi sata. Mu ne nan muka yi sata a gidan Alhajin garin nan da gidan Alhajin Damaturu…..”
Ba ya ga surutan, sai kuma a ga ya tashi yana ta tikar rawa haikan, ga gumi na ta malala a jikinsa. Mutane na ta al’ajabi, wasu ma na zub da hawaye, ganin irin halin da Shugaban ‘yansintirin ya sami kansa na tabin hankali cikin kankanin lokaci. Ammm da DPO ya kammala jin ta-bakin Matar Alhaji cikin sirri, sai aka ga ya kira wani katon kurtun dan sanda tutturna ya ba shi umarni kamar haka;
“Ka dauki wancan kulkin, ka karanta Ayatal Kursiyyu kafa guda ka tofa a kulkin, sannan sai ka kantara masa a gadon baya (ya nuna Tanimu cikin fushi). Ka yi haka kamar sau goma sha-biyu, da yardar Allah, yanzun nan ba da jimawa zai dawo cikin hayyacinsa”
Jin haka, sai jama’ar dake wurin suka ce;
“Haba Yallabai! Ai ba a yin rukiyya da kulki”
Ya amsa da;
“Amma dai kun san ilmi kogi ne ko? Ku bar gani na haka cikin kakin ‘yansanda, daga Gidan Makaranta na fito, kuma na yagi abin da na yaga bakin gwargwado na karatu. Na lura Aljanun da ke jikinsa girda-girda ne, wannan ‘yar bulalar ta Malam, jin ta suke a jikinsu tamkar sakace ne ma ake musu. Amma wannan salon addu’ar da na canja yanzun nan zai haifar da kyakkyawan sakamako da yardar Allah…..”
Tanimu ya shanye kulki uku yana mai sa-ran jama’ar da ke wurin za su shawo kan DPO a daina kantara masa kulki, amma sai ya fahimci cewa bayanan da DPOn ya yi ya gamsar da su. Har ma wani cikin jama’ar na cewa;
“Tun da haka ne yallabai, me zai hana ya zamana ‘yansanda biyu ne a kansa kowa da nasa kulki, saboda hakan zai gaggauta korar iskokan daga cikinsa?”
Gabanin Tanimu ya ji amsar da DPO zai bai wa wannan mutumi, sai aka ga ya zabura yai tsalle yana fadin;
“Don Allah yallabai ka yi min rai zan fadi gaskiya”
Wadanda ba su san dawan-garin ba, sai murna ta kama su suna fadin;
“Barka barka Tanimu, Allah Ya dora ka a kansu. Allah Ya kara maka lafiya. Ka tsaya a karasa maka sha-biyun, ta yadda Iskokan za su rabu da kai fanfanfan. Daga yin bakwai har ka fara dawowa hayyaci, da ma Yallabai ya fada”
Mai rukiyya ya nemi zai je ya kama-ruwa, amma sai aka ga Tanimu ya kamo cunar rigarsa yana cewa;
“Wallahi Allah har da shi. Shi ma barawon ne”
Sai aka tuntsure da dariya, wasu na cewa;
“Amma dai Wallahi aljanu ‘yan kalen sharri ne, wai ma malamin barawo ne. Shegu masharranta. Don Allah yallabai a cikashe masa sauran kulakan don ya kara wartsakewa”
DPO cikin murmushin keta, yai wa wannan kurtun wata inkiya, ji kake wani tuuuummmm! tuuuuuummmmm! Ya cigaba da jubdar Tanimu. Ganin ba Sarki sai Allah ne, sai Tanimu ya sake tsala ihu har da fitsari, sannan ya durkusa yana mai kama kafar DPO yana hada shi da girman Allah da Annabi ya sassauta masa zai fadi gaskiya. Ganin haka, sai matarsa tai bakin kofa tana kokarin arcewa. Tanimu ya riko kafarta yana mai cewa ita ma barauniyar ce, amma ta-zaune.
Wannan yanayi ya sanya jama’ar da ke wurin suka shiga salallami. A karshe, DPO ya fada musu cikakkun bayanan da ya samu wajen Matar Alhaji. Sannan, Shugaban ‘yansintiri ya gaskata zargin da matar Alhaji tai masa.
Bayan kammala bincike, ‘yansanda suka kai Tanimu kotu aka yanke ma sa hukunci mai tsanani da ya kunshi zaman gidan yari da biyan tara mai yawa saboda cin amana da ha’incin da ya yi alhali an amince ma sa a cikin al’umma.


Advertisement
Click to comment

labarai