Connect with us

WASANNI

Ana Rububin Sayen Rigar Ronaldo Ta Juventus

Published

on


Daruruwan magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus na ta yin tururuwa domin siyan riga mai dauke da lamba bakwai da kuma sunan Cristiano Ronaldo a jiki bayan da dan wasan yakoma kungiyar a wannan satin.
Magoya bayan sun dukufa wajen rububin ne, yayinda kungiyar ta Jubentus ke shirin tabbatar da zuwan sauyin shekar Ronaldo zuwa gare ta a hukumance, ranar Litinin mai zuwa.
Kafin wannan lokaci dai, Juan Cuadrado ne ke sanyawa kungiyar riga mai lamba bakwai tun bayan sauyin shekar da ya yi daga Chelsea a shekarar 2015, amma halin yanzu hakan na nufin Cuadrado zai rasa lambarsa kenan sakamakon zuwan Ronaldo,
A farkon wannan mako, Jubentus ta tabbatar da sayen Ronaldo daga kungiyar Real Madrid kan kudi euro miliyan 100, inda zai rika amsar albashin euro miliyan 30 a duk shekara, sabanin euro miliyan 23 da ya ke karba a Real Madrid.
Tuni dai Ronaldo ya tabbatar da komawarsa Jubentus a wata wasika daya rubutawa magoya bayan Real Madrid inda ayke musu godiya da irin goyon bayan da suka nuna masa tun bayan komawarsa kungiyar.


Advertisement
Click to comment

labarai