Connect with us

LABARAI

An Kaddamar Da Shirin Raba Magani Kyauta Ga Jarirai A Kebbi

Published

on


A jiya ne Ma’aikatar kula da Lafiya ta jihar kebbi tare da hadin guiwar ofishin UNICEF da ke a jihar Sakkwato suka kaddamar da shirin bayar da sinadarin Bitamin ga kananan yara a kyauta a jihar kebbi .
Bukin kaddamar da shirin an gudanar da shi ne a dakin taro na makarantar koyon aikin jinya da kuma unguwar zoma wato” school of Nursing and midwibes” da ke Birnin-kebbi. An kuma gaiyato iyayen jarirai sababbin haihuwa tun daga haihuwa zuwa kwanaki dubu daya na haihuwarsu, domin fadakar dasu da kuma horas da su ta musamman, kan yadda zasu ba ‘ya’yansu madarar mama har tsawon wata shida ga jariransu domin gudun kamuwa da ciwon tamuwa ga jariran nasu.
Haka kuma a wurin taron an gabatar da hotunan bidiyo ga wadanda aka gaiyato domin ganin irin yadda ake amfani da sinadaran Bitamin da kuma irin abincin da ya kamata a ba yara bayan kwanaki dari da haihuwarsu.
Har ilayau jami’an da suka gabatar horarwar sun hada da mista Uruakepa John daga ma’aikatar kiyon lafiya ta tarayya wanda kuma mataimakin Darakta ne da ma’aikatar da kuma mis Beatric Kware jami’ar kula da harkar tamuwa a ma’aikatar kiyon lafiya ta jihar kebbi inda suka yi kira ga masu ruwa da tsaki, dangane da al’amarin kiyon lafiya , shuwagabannin addinai da kuma Sarakunan gargajiya da kuma shuwagabannin kananan hukumomin da ke a cikin shirin, don tabbatar da cewa ba’a karkatar da madarar sinadaran Bitamin da aka basu a kyauta domin amfani da madarar kamar yadda ya kama ta.
Buga da kari kuma sun kara cewa “ wannan shirin da aka kaddamar na kananan hukumomi uku ne daga cikin ashirin da daya da ake dasu a cikin jihar ne suka samu shiga, cikin shirin da gwamatin tarayya ta fito dashi karon farkon a jihar ta kebbi, na bayar da madarar sinadaran Bitamin ga jarirai a kananan hukumomin Birnin-kebbi, Jega da kuma Danko Wasagu, da ke jihar ta kebbi a jiya wanda matar Gwamnan jihar Dakta Zainab Bagudu ta jagoranci shirin a jihar ta kebbi, wanda babbar sakatariyar ta ma’aikatar kiyon lafiya ta jihar Hajiya Halima Boye Dikko ta wakilta a wurin bukin taron da aka gudanar a dakin taro na makarantar koyon aikin jinya da kuma unguwar zoma ta jihar.
Da take gabatar da jawabin ta a wurin taron matar Gwamnan jihar Dakta Zainab Atiku Bagudu, ta bayyana jin dadinta akan irin kokarin da masu ruwa da tsaki keyi, da kuma gudunmuwar da suke bayarwa wurin ganin cewar jihar kebbi, ta ci gaba kan harkar kiyon lafiya. Ta kuma tabbatar masu da cewar gwamnatin jihar kebbi zata ci gaba da bada nata goyon bayan kan harkar kiyon lafiya ga al’ummar jihar ta kebbi.
Haka kuma tayi kira ga Sarakunan gargajiya, shuwagabannin addini , shuwagabannin kananan hukumomi, da kuma sauran masu ruwa da tsaki kan harkar kiyon lafiya na ckin jihar dasu taimaka wurin ganin cewar wananan shirin ya samu nasara da kuma tabbar da cewa ba’a, karkatar da akalar madarar sinadaran Bitamin da aka kawo a jihar domin ba jariran kananan hukumomin uku da suka samu shiga cikin shirin a karo na farko.
Daga karshe dai ta godewa jama’ar da suka halarci bukin kaddamar da bada madara sinadarin Bitamin B, da kuma shuwagabannin kananan hukumomi jihar ta kebbi kan irin kokarin su, na ganin cewaR wananan shirin ya samu nasara a jihar kebbi.


Advertisement
Click to comment

labarai