Connect with us

LABARAI

Rundunar ’Yan Sanda A Kano Ta Aike Wa Sanata Gaya Da Kawu Sumaila Sammaci

Published

on


Sakamakon fito na fito da akayi tsakanin magoya bayan Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da Magoya bayan Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin Majalisar Honarabul Abdurraham Kawu Sumaila a lokacin kaddamar da sabun aikin titin Kano zuwa Abuja wanda akayi a garin chiroma a kwanakin baya,  yanzu haka rundunar ‘yan sandan Jihar Kano karkashin Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano Alhaji Rabiu ta yi Sammacin Sanata Kabiru Gaya da Kawu Sumaila domin su gurfana a gabanta domin kamo bakin zaren warware wannan matsala ta dabanci da take habaka a halin yanzu a Kano.

Bayanin Hakan ya fito daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ASP Magaji musa Majiya alokacin da yake bayyanawa duniya wannan aniya ta rundunar ‘yan sanda,  yace ranar Asabar data gabata ne  aka fara zama da Kawu Sumaila guda cikin wadanda aka gayyata ya yinda Sanata Kabiru Ibrahim Gaya bai samu halartar ganawar ba sai wakilci da ya turo, wanda kuma aka dage zaman zuwa Juma’a mai zuwa domin gudanar wannan zaman domin lalubo bakin zaren hana magoyan bayan fito na fito  da muggan makamai kamar yadda aka gani alokacin waccan taro.

Shi dai wannan zama daga cikin wadanda aka gayyata har da shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Honarabul Abudullahi Abbas, tuni dai jama’ar Kano irinsu makusanacin Gwamanan Kano kuma makusancin Shugaban kasa Alhaji Danbalki Kwamanda ke kokawa da yadda yake zargin Gwamnati Kano ta yanzu da bunkasa harkar daba a tsakanin matasan Jihar Kano.

Idan dai ana biye da halin da siyasar Kano ta Kudu ke ciki ahalin yanzu, an san yadda tukunyar siyasa a wancan bangare ke kara tafarfasa sakamakon yadda wadancan mutane biyu Sanata Gaya da Kawu Sumaila kowanne ke kokarin ganin sai ya mallaki waccan kujera ta Sanatan Kano ta Kudu, wanda shi Sanata Gaya yanzu yake cikin zango na uku akan wannan kujera.

Hakan ta sa magoya bayan Kawu Sumaila ke ganin lokacin ya yi da ya kamata a samu canji domin acewarsu Kabiru Gayan ya gaza samar da abubuwan da ake bukata a wancan yanki.


Advertisement
Click to comment

labarai