Connect with us

LABARAI

Nijeriya Ta Sake Mayar Da Martani Kan Rahoton Amnesty Kan Take Hakkin Dan Adam

Published

on


Nijeriya ta sake yin watsi da rahoton hukumar neman afuwa ta duniya, ‘Amnesty International,’ wanda take zargin Sojojin kasarnan da kisan mutane ba bisa ka’ida ba.

Gwamnatin ta tarayya ta ce, ba ta taba kare kanta ba daga rahotannin da kungiyar ta Amnesty International, ke bayar wa na take hakkin dan adam a kasarnan.

Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja, lokacin da tawagar hukumar kare ‘yancin dan adam ta kasa, karkashin jagorancin babban sakataren hukumar, Tony Ojukwu, ta kai ma shi ziyara.

Mun sha kawo maku rahotannin da ke nu ni da yadda ake ta samun takun saka tsakanin kungiyar ta Amnesty da kuma rundunar Sojin ta Nijeriya kan irin rahotannin da Amnesty din ke fitarwa da ba sa yi wa Sojojin dadi.

Na baya-bayan nan shi ne wanda aka yi wa take da, “Sun yaudare mu: An yi wa matan da suka tsira daga hannun Boko Haram fyade, aka barsu da yunwa aka kuma tsare su a Nijeriya,” wannan rahoton ya janyo cece-kuce a tsakanin Amnesty din da Sojojin.

Da take mayar da martani kan wannan rahoton ta bakin daraktan ta na yada labarai, Birgediya Janar John Agim, shalkwatar ta rundunar Sojin, cewa ta yi, Amnesty tana son kawo rudami ne a kasarnan ta hanyar bayar da wannan rahoton nata.

“Ba wai muna kokarin mu kare kanmu ne ba gabadaya, ba cewa muke yi sam ba mu da wani laifi ba, domin ai ba wata kasar da ba ta da laifi sam-sam.

“Sai dai, muhimmin abu a nan shi ne, mun san mahimmancin kare hakkin dan adam, muna kuma bakin kokarinmu a kan hakan, domin ganin duk dan Nijeriya ba a take masa hakkinsa ba.

Ministan ya ce, gwamnati ta gwammace ta karbi duk wata suka ta kuma yi aiki a kanta, da a ce ta fito tana kare kai ne.

A cewarsa, kungiyoyi masu zaman kansu na ciki da wajen kasarnan ba su fi gwamnatin Nijeriya damuwa da hakkokin ‘yan Nijeriya din ba.

“Muna da nufin ganin ‘yan Nijeriya suna more kowane irin hakkin su na dan adam.

“Gwamanti ba ta bakin cikin hakan. A duk lokacin da muka sami irin wannan rahoton, mukan duba mu gani.

“Mukan tara dukkanin sassan Jami’an tsaronmu mu binciki kanmu don mu ga inda muka kasa, da kuma yadda za mu gyara lamarin,” in ji Ministan.

Ya ce Nijeriya ce kan gaba wajen kin a yaki kotun aikata laifuka ta duniya, ICC, kamar yadda wasu kasashen Afrika ke son yakar ta.

Ya yi nu ni da yadda kasashen afrika da yawa suke ta kiran da a fice daga cikin wakilcin kotun ta duniya, bisa zargin da suke yi na cewa, wai ta fi mayar da hankali ne kadai kan shugabannin na Afrika.

Ministan ya ce, Hukumar ta kare hakkin dan adam, NHRC, tana da matukar mahimmanci a duniya, kamar yadda take da mahimmanci ga wannan gwamnatin ta Shugaba Buhari, da kuma ma’aikatar ta harkokin waje.

Da yake magana tun da fari, babban sakataren cewa ya yi, sun kawo ziyarar ce ma’aikatar domin neman hadin kai wajen aiwatar da ayyukan hukumar ta NHRC.

Ya ce, a wasu lokuta hukumar na su takan sami rahotanni kan lamurran ‘yan gudun hijira da kuma koken da suka shafi harkokin waje, wanda suna da bukatar sanya bakin ma’aikatar ta harkokin wajen.

“A baya, yanda muke yi kan irin wadannan koke-koken shi ne, mukan sami wani jami’in ma’aikatar ta harkokin waje da kai tsaye muke tura su gare shi domin daukan mataki a kan lokaci,” in ji Sakataren.

Daganan kuma ya nemi hadin kan ma’aikatar wajen samawa jami’an hukumar dukkanin takardun izinin da suka dace a duk lokacin da jami’an hukumar suka so fita wajen kasarnan domin halartar taruka.

 


Advertisement
Click to comment

labarai