Connect with us

LABARAI

Kungiyar Matasan Kano Sun Kubutar Da ’Yan Gidan Yari Goma

Published

on


Kamar yadda kungiyoyi da al’umma ke kai ziyara gidajen yari da gidajen marayu da asibitoci da sauransu, ita ma kungiyar nan dake Kano mai suna kungiyar matasa da ‘yan uwan juna da marasa galihu ta kai irin wannan ziyara a daya daga cikin gidan yarin na Kano dake Gorondutse.

Kamar yadda shugaban kungiyar na kasa baki daya Malam Ali Musa ya shaidawa manema labarai kwanakin baya jin kadan da kammala taron da suka saba gudanarwa lokaci lokaci. Malam Ali Musa, ya kara da cewa, a ziyarar da suka kai sun kai ma daurarrun kayayyakin bukatar yau da kullum na dubban nairori.

Bayan haka kuma inji shugaban sun kubutar da fursunoni kimanin mutane 10 ta hanyar biya masu taran kudade, sannan har ila yau sun baiwa kungiyar musulmai na gidan yarin tallafin Naira dubu 50 domin su sanya a cikin asusun kungiyar domin tallafa wa duk wani mai bukata ta musamman daga cikin Fursunonin, sakamakon koken da shugaban kungiyar gidan ya yi masu na rashin kudi a cikin lalitan kungiyar.

Bayan wannan ziyaran da suka kai gidan Yarin na Gorondutse sun kai irin ta gidan marayu dake Nassarawa nan ma sun kai masu kayayyakin abinci da takalma da sabulan wanka da wanki tare da kayan sawa. Hatta irin wannan taimako sukan ba da shi daga cikin ‘yan kungiyar musamman idan suka lura da haka mace kona miji.

Shugaban kungiyar ya ce suna samun kudaden tafiyar da aikace aikace kungiyar ne ta hanyar sanya haraji ga duk wanda yake kungiyar, kuma kungiyar tasu tafi karfi ne a jihar Kano, tana kuma da mambobi daga jihohin Katsina da Kaduna da Jigawa da Yobe da Maiduguri da Gombne. Sannan kuma sun yi wa kungiyar rajista domin jin dadin tafiyar da aikace aikacen kungiyar .

Daga karshe ya roki gwamnatocin kasar nan dasu mayar da hankali wajen taimaka wa kungiyoyin da bana gwamnati ba ganin yadda suke taimakawa rayuwar al’umma da ci gabansu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai