Connect with us

LABARAI

Kimiyya Da Fasaha Muhimmai Ne Wajen Samar Da Ayyukan Yi –Minista

Published

on


Ministan kimiyya da fasaha, Dakta Ogbonnaya Onu, ya ce, matukar kasarnan za ta alkinta hazakar da take da shi a fannin kimiyya da fasaha, tabbas za ta sami karuwar arziki da ayyukan yi, za kuma ta rage talaucin da al’ummanta ke fama da shi.

Onu ya ce, wannan gwamnatin mai ci yanzun, ta fahimci amfanin kimiyya da fasaha da kuma kirkire-kirkire, da kuma sanya matasa, kwararru, ‘yan kasa da ‘yan kwangila a kan hakan yadda ya kamata, domin ganin bunkasar kasarnan.

“Daga yanzun, Nijeriya za ta kara habaka dimbin albarkatun kasarta ne ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasaha da kuma sabbin kirkire-kirkire, domin sarrafa abubuwan da muke da bukatar su a cikin gida, wanda hakan zai samar mana da dukiya mai tarin yawa, ya samar mana da ayyukan yi, ya kuma rage mana radadin talauci,” duk Ministan ya fadi hakan ne a Legas wajen wani taro.

Ministan ya ce, “Matukar za mu yi amfani da abin da muka karanta na kimiyya da fasaha a wajen gina kasarmu, tabbas akwai haske mai yawa ga wannan kasar tamu. Dokar gwamnati ta biyar, tana nufin, sanya kishi ne da kuma son kasa.

“Gwamnatin Buhari tana sa ran nan da shekaru 10 zuwa 20, kamfanonin Nijeriya za su rika yin takara ne da mafiya kyawu na takwarorinsu da ke wajen kasarnan, wajen gabatar da ayyukan kwangila da sauran aikace-aikace.

Ya ce wannan dokar ta yi umurni ne da bayar da ayyukan kwangila ga kamfanonin ‘yan kwangilarmu na nan cikin gida, kamar yadda dokar bayar da ayyuka ta shekarar 2007 ta bukata.

Onu ya kara da cewa, “Tun da dai a yanzun kamfanoninmu na ‘yan kasa suna da dama fiye da a baya, na shigan su cikin ayyukan habaka kasa, ta hanyar ayyukan kwangilolin da ake ba su. sam dadewan kamfani ba shi ne a gabanmu ba, matukar dai kamfanin ya cancanta yana kuma da dukkanin rajistan da ta dace, zai kuma iya yin aikin da aka ba shi yadda ya kamata.

“Daga yanzun, gwamnati za ta fi mayar da hankali ne kan kwararrunmu na nan cikin gida da kamfanoninsu, wajen zayyanawa da kuma aiwatar da kowane irin aiki da ya shafi tsaron kasa. Za mu kawo kwararru daga waje ne kadai a inda ba mu da kamar su a nan Nijeriya.

“Kuma ko mun kawo su, za mu hada su ne tare da namu kwararrun na nan cikin gida. Hakanan dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati an umurce su da su fi mayar da hankali ne ga kwararrun namu na nan cikin gida, domin hakan zai karfafa wa kwararrunmu da ke zaune a waje gwiwar dawowa cikin kasar su, su ciyar da ita gaba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai