Connect with us

LABARAI

Ban Yi Nadamar Safarar Alburusai 20,000 Nijeriya Ba –Anokwara

Published

on


An kama wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ‘yan fasa kwari ne da albarusai 200,000 masu rai, a kan hanyar iyakar Wawa-Babana a Jihar Neja.

Rundunar shiyya ta hukumar Kwastam mai kula da Jihohin, Neja, Kwara da Kogi ne suka yi kamun.

Mutanan da ake zargin, Martin Anokwara da Bukari Dauda, rundunar ta kwastam mai kula da kan iyakar ne na Jihar Neja da Jamhuriyar Benin ta kama su.

Majiyarmu ta ce, wadanda ake tuhuman sun taso ne daga jamhuriyan ta Benin cikin babbar mota shake da kwanson albarusai 200,000 zuwa garin Onitsha, ta Jihar Anambra.

Daya daga cikin mutanan da ake tuhuman mai suna Mista Anokwara, ya shaida wa manema labarai cewa, ya tafi jamhuriyan ta Benin ne domin sayo albarusan domin ya sayar wa mafarauta da masu bindigogin da ke da lasisi a shiyyar kudu maso gabacin kasarnan.

“Ba domin a yi fashi da su na kawo su ba, ina sayarwa da mafarauta ne a Jihar da nake da kuma sauran Jihohin gabashin kasarnan, na kuma jima ina kawo wa mutane su. Ban san za a kama ni ba, daman haka rayuwa take, duk hakan na cikin kalubalen rayuwa.

“Daman rayuwa ai kalubale ce, ba zan ce na yi nadaman hakan ba, saboda na san abin da nake yi, ba kuskure ne ba. Ko ma dai mene ne, a bari doka ta yi aikinta,” in ji Mista Anokwara.

Direban babbar motar, Dauda, ya shaida wa manema labarai cewa, shi bai san abin da ke cikin motan ba, shi dai an dauke shi hayan tuko motan ne kawai daga Kotono zuwa Onitsha.

Kwamandan shiyyar, Benjamin Binga, cewa ya yi, mutanansa ne suka kama motar wacce ta shigo cikin kasarnan ta kan iyakan Babana da misalin karfe 3 na safiyar Litinin.

Benjamin Binga, ya ce, babbar motar ta yi bad da kama ne da jarkokin da babu komai a cikinsu sama da 100, amma da aka bincika sai aka gano akwai wata barauniyar ma’ajiya a kasar motan inda aka boye albarusan.

“Ba wai an ba mu satar amsa ne a kan motar ba, mutane na ne dai suka yi aikinsu a cikin natsuwa, har sai da suka gano wannan almundahanar da aka shirya a kasar motar, inda suka gano albarusan.

“Albarusan dubbai ne, za mu yi awanni muna kirgan su. Yanzun dai muna kokarin gano abin da ake son yi ne da albarusan, da kuma wanda ya turo a kawo su cikin kasarnan,” in ji shi.


Advertisement
Click to comment

labarai