Connect with us

LABARAI

Sabon Salon Farmakin Giwaye Daga Dajin Yankari, Mutane Biyu Sun Mutu Guda Ya Raunana Kauyuka Sun Razana

Published

on


A ranar lahdin da ta gabata ne mazauna wasu yankuna a karamar hukumar Alkaleri da ke cikin Jihar Bauchi suka gamu da farmakin giwaye da suka fito daga gandun dajin shakatawa na Yankari inda suka rika bin mazauna wasu kauyuka kimanin biyar dake kusa da dajin yadda suka kashe mutane biyu suka kuma raunana mutum guda, daga bisani kuma wasu mazauna yankunan suka yi hijira saboda da tsoron da  ya shiga zukatan su a sakamakon farmakin giwayen.

Mazauna yankunan Gortan Bali da Busalla sune suka fi jin radadin farmakin giwayen saboda kashe mutanen su guda biyu daya magidanci mai mata da yara wanda ake kira Malam Haruna Jaudo wanda giwayen suka kawo hari gonar sa suka rufa shi da gudu amma daga bisani ya gaza giwayen suka tattake shi ya mutu a kusa da garin Busala. Daga nan kuma suka wuce inda suka dumfari garin Gorton Bali kafin shiga garin suka iske wani manomi mai suna Malam Musa Mustapha shima suka kai masa hari suka kashe shi. Bayan mazauna garin sun fito da ihu da sauran dabaru suka kora giwayenn zuwa gaba.

Harin wanda giwayen suka kai shi cikin kankanen lokaci wanda aka yi daga karfe biyu na rana zuwa karfe uku a lahdin da ta wuce, giwayen sun sake wucewa  zuwa yankin Yalwan Duguri wanda shima wajene mai dausayi inda suka iske Malam Ahmed Shehu a gonar sa suka rufa shi da gudu ganin zai kasa ya samu hayewa kan wata babbar bishiya inda a sakamakon hakan shima ya samu raunuka ya kuma buga kan sa yadda bayan wucewar giwayen aka kai shi asibitin Yalwan Duguri aka yi masa jinya kamar yadda jami’in asibiti Baba Black ya shadawa manema labarai cewa ya razana kuma ya samu rauni a kan sa, amma da sauki shi yasa suka sallame shi zuwa gida inda ke ci gaba da jinya.

Giwayen daga lokaci zuwa lokaci sukan fito har kan hanyar Bauchi zuwa Gombe kuma basu cika yin barna wa mutane ba sai ko lalata amfanin gona amma a bana sun raunata mutane tare kashe magidanta biyu lamarin da ya fara sa tsoro a zukatan mutanen yankin. Inda Alhaji Ibrahim Sarkin yakin yalwan Duguri ya bayyana wa manema labarai cewa tuni sun rubuta ruhoto zuwa karamar hukumar Alkaleri daga can kuma za a tura Bauchi don ci gaba da bincike tare da samo hanyoyin kariya ga jama’ar yankin daga farmakin giwayen  da ke aukuwa daga lokaci zuwa lokaci.

Alhaji Ibrahim Sarkin yaki ya yaba game da kokarin jami’an lura da gandun dajin Yankari saboda ganin kokarin da suka yi na shawo kan giwayen inda suka korasu zuwa cikin dajin na Yankari kafin daga baya suka kwaso gawarwakin mutanen biyu suka mika su ga iyalen su aka yi musu jana’iza.  Don haka ya bayyana cewa za su  ci gaba da fadakar da gwamnati game da yadda za a taimakawa mutanen yankin don su fita daga halin dimuwa da suka shiga game da wannan farmaki na giwaye da ya fara daukar sabon salon salwantar da rayukan jama’a wanda a baya ba a saba ganin hakan ba.

Malam Juji Haruna Muazu Dimis jami’in watsa labarai na karamar hukumar Alkaleri ya labartawa wakilin mu cewa akwai hanyoyin da giwayen ke bi wadanda suka tashi daga Yalwan Duguri zuwa Dimis zuwa Gorton Bali zuwa Kumbala da sauran yankunan da a halin yanzu mutane suka fara razana da halin da aka shiga musamman ganin yadda giwayen suka sake salo a duk lokacin da  garken su  ya fito suna bin duk wani mutum da suka hango har sai sun cim masa. Don haka ya bayyana cewa wannan ruhoto ya samu karamar hukumar Alkaleri kuma tuni sun tura zuwa Bauchi don a san irin matakin da za a dauka don kare rayukan mutanen yankin.

Dukkan kokarin da wakilin mu ya yi don ji daga bakin kantoma mai lura da gandun dajin na Yankari Injiniya Habu Mamman ya ci tura, saboda yawanci idan ana dajin wasu lokuta ana samun matsalar kama layin wayar tarho, amma duk lokacin da muka ji daga gare shi za mu sanar da masu karatu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai