Connect with us

LABARAI

Mun Samo Naira Biliyan 2.8 A Bodar Seme –Kwastan

Published

on


Hukumar Kwastam na yankin iyakan kasar nan ta Seme, sun sanar da karbar harajin Naira 2, 861,342,694.00 tsakanin watan Janairu zuwa watan Yuni na shekarar 2018.

Hukumar ta kuma sanar da kwace kayayyaki nau’i 620 wanda kudaden harajinsu ya kai Naira 432, 930,517.00 a tsakanin lokacn da ake nazarin.

A sanarwar da jami’in watsa labaran hukumar, Saidu Nuruddeen Abdullahi, ya raba wa manema labarai a Legas ranar Litinin, ta ce, shugaban yanki na Kwastam ‘Customs Area Controller (CAC)’ Mohammed, Aliyu, ya bayyana cewa, wadannan harajin da aka samu sakamakon hadin kai ne da jajircewa da aka samu daga dukkan masu ruwa da tsaki da kuma jami’an Kwastam wajen kokarin gudanar da aiyyukansu.

Ya ce, an samu wannan nasarar ne duk da faduwa da karancin shigo da kayayyki da ake das hi ta iyakan kasar nan.

Kwantrolan ya kuma tabbatar da kudurinsa na yaki da fasa kwauri gaba daya, ta hanyar samar da tsare tsare da hanyoyi daban daban don fuskantar hayoyi daban daban da masu fasa kwauri ke bullowa dasu a kullum wajen yi wa kasa zagon kasa ta hanyar shigo da kayyakin da aka haramta ta barauniyar hanya.

A wata sabuwa kuma, Kwantrolan, ya bayyana wa wasu shugabannin dalibai da suka kawo masa ziyara cewa, ya kamata duk fasinjan da suke shigowa cikin kasar nan su sani cewa, bai kamata su bar sansanin da ma’aikatan Kwastam ke bincike ba, ba tare da an bincikesu tare da tabbatar da basu dauke da wani abu dake da matsala ba, ya kuma bukaci masu amfani da hanyar na data taso daga Legas zuwa Abidjan dasu ci gaba da bai wa jami’an Kwastam hadin kai a aikin da suke gudanarwa.


Advertisement
Click to comment

labarai