Connect with us

LABARAI

Matsafa Sun Tono Gawa Tare Da Yanke Kanta A Neja

Published

on


An gurfanar da wasu mutane goma a gaban kotun majistare ta 1 da ke garin Minna, wadanda ake zargi da hada baki da tono gawa daga makabarta, sannan suka yanke kanta, da nufin yin tsafi.

Ana tuhumarsu ne da aikata laifuka hudu na, hada baki a aikata laifi, rashin tona asirin aikata laifin, mallakan kan dan adam da kuma shiga makabarta ba tare da izini ba. Wanda duk hakan ya sabawa sashe na 97D2d, 138, 213 da 219, na dokar Fenal Kod.

A bisa takardar gabatar da kara kan aikata laifin, Jaridarmu ta jiwo daga garin na Minna cewa, a ranar Litinin, Salihu Mohammed, Nma Alhassan da Kolo Alhaji Isah, an yi zargin sun shiga makabartar Musulmi ta Mangorota, ta garin Lemu, da ke karamar hukumar Gbako, ta Jihar, a ranar 18 ga watan Yuni 2018.

Su ukun, ana zargin sun tono gawar wata mai suna, Hajiya Aisha Tetengi, suka yanke kanta da nufin za su yi tsafi da idandunanta, sai suka bar gangar jikin a wajen.

Rahoton ya ce, wani mai suna, Alhaji Abdullahi Abdulateef, na garin Bama, ya kai rahoto a ofishin ‘yan sanda da ke Bida, inda yake cewa, Salihu Mohammed da Nma Alhassan na kauyan Mongorota, ya yi ma shi waya yana yi masa tallar kan mutum.

Nan take ‘yan sanda suka ce sai suka shiga aikinsu, wanda a lokacin binciken nasu ne, Yahaya Idris da Mohammadu Buhari, sun sami Mohammed Jiya, a gidan Alhaji Adamu Abubakar, inda suke neman idon mutum daga gare shi domin su yi tsafi.

Rahoton ya ci gaba da cewa, Adamu Abubakar sai ya tuntubi Mohammadu Alfa wanda shi kuma ya tuntubi Abdulkadir Malam Isah Masaga shi kuma ya yi wa Mohammed Baba Anfani, magana,  daga nan shi kuma ya hada shi da Salihu Mohammed da kuma, Nma Alhassan da Kolo Alhaji Isah.

A cewar rahoton, Salihu Mohammed, Nma Alhassan da Kolo Alhaji Isah sune suka dauki kan matan da aka yanko zuwa wajen Malam Mohammadu Alfa, wanda a wajen ne ake zargin cewa ‘yan sanda sun gano kan.

“A lokacin binciken, ta bayyana cewa, duk kun hada baki a tsakaninku, da gangan, ku ka kuma ki ku kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda kan aikata laifin, duk kuma kun yi ikirari da aikata laifin,” in ji rahoton.

Mai shari’a, Alhaji Muhammad Gimba Gaba, ya karanta wa wadanda ake tuhuman laifukan nasu hudu da ake tuhumansu da su, inda duk suka musanta hakan.

Alkalin ya yi umurni da a mayar da wadanda ake tuhuman gidan Yari, sai ya daga shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Yuli, domin ci gaba da sauraren batun neman belin da aka yi.


Advertisement
Click to comment

labarai