Connect with us

LABARAI

Jam’iyyar APC Ce Maganin Matsalolin Shekara 4 Da Aka Fuskanta A Jihar Ekiti – Tinubu

Published

on


Jagora kuma jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci al’ummar jihar Ekiti dasu fito kwansu da kwarwatarsu wajen kada wa jam’iyyar kuri’a a zaben gwamna da zai gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Bola Tinubu ya ce, jam’iyyar APC ce magani kuma waraka ga shekaru 4 da aka yi a cikin kunci da rashin cika alkawari da talaucin daya addabi jihar tun da gwamna Ayodele Fayose ya dare karagar mulki a shekarar 2014.

Tinubu ya yi wannan bayanan ne a wata tattaunawa daya yi a garin Ado-Ekiti ranar Litini, ya kuma kara da cewa, jam’iyyar APC ce kadai za ta iya bunkasa dukkan fannonin rayuwar ‘yan Nijeriya gaba daya. A na sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai isa jihar Ekiti ranar Talata inda ake sa ran zai gana da sarakuna gargajiya da shugabannin jam’iyyar APC da kuma magoya bayan jam’iyyar, zai kuma halarci babban taron yakin neman zaben jam’iyyar tare da gabatar da dan takarar gwamna na jam’iyya Dakta Kayode Fayemi, a shiye shiryen gudanar da zaben gwamna da za a gudanar ranar Asabar a fadin jihar.

Tinubu ya ci gaba da cewa, “Muna matukar godiya ga jama’ar jihar Ekiti a bisa karamci da mutumci da suka nuna mana tunda muka shigo.

“Mu shugabanin jam’iyyar APC, muna mautukar gaisheku a bisa hakuri da kuka yi da mummunan mulkin danniya da jam’iyyar PDP tayi muku na tsawon wannan lokacin kafin zuwan jam’iyyar APC a karagar mulkin gwamnatin tarayya da kuma shirn kafa mulkin jam’iyyar APC da ku keyi a jihar Ekiti.

“An yi mana mulkin shekara 16 na danniya da rashin mulki na gari da korafe korafe dangane da tattalin arziki da rashin ci gaba da kuma mulkin rarraba kan jama’a.

“Wadannan gubatacciyar mulkin shekara 16 na jam’iyyar PDP, Allah ne Ya taimaka mana da zuwan mulkin jam’iyyar APC a gwamnatin tarayya da kasar nan ta ruguje gaba daya.

“Sauran jihar daya rage shi ne jihar Ekiti. A kan haka muke kiranku daku jefa wa dan takararmu Dakta Kayode Fayemi, na jam’iyyar APC a zaben ranar Asabar, shi mutum ne tsayayye da zai iya kawo canji daya kamata a jihar Ekiti.”

A kan haka ne, mu shugabannin jam’iyyar APC na kasa ke tsayawa da kuma yi muku al’kawarin lallai jihar Ekiti za ta samu ci gaba a dukkan fannin rayuwa in har kun zabi Dakta Kayode Fayemi a matsayin gwamnan jihar Ekiti.”

Tsohon gwamnan ya kuma tunatar da matasa a kan fuskantar ci gaban rayuwarsu, dole ku fuskanci rayuwarku kuma gwamnan nan namu ne gaba daya.

“Jam’iyyar APC ta yi kyakyawar shiri don raywarku saboda haka kada ku sayar da rayuwarku a kan kudi dan kalilan, kada ku jinginar da rayuwarku gaba daya.

“Kada ku yarda wani ya yi muku barazana ya hana ku sauke nauyin dake kanku na jefa kuri’a, tsitsiya alamu ne na hadin kai.

A wata tattaunawa da aka yi da tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande, ranar Asabar, ya ce, lallai zabe da za a gudanar ranar Asabar, ya zama dole jam’iyyar ta lashe saboda bai kamata jam’iyyar ta zama jam’iyyar adawa a yankin yammacin kasar nan ba.

“lallai za a gudanar da zaben ranar Asabar lami lafiya, lokaci ya yi da dukkan ‘yan kabilar Yarbawa zasu hada kai a kan wannan zaben. Bai kamata mu bar kanmu a bangaren ‘yan adawa ba, lallai jam’iyyar APC za ta lashe zaben ranar Asabar,” inji shi.

An shirya gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti a kananan humomini 16 na jihar ranar Asabar yayin da za a rantsar da duk wanda ya lashe zaben a ranar 16 ga watan Oktoba na wannan shekarar.

Baya ga Tinubu da Akande da suka iso jihar ta Ekiti kafin isowar shugaba Buhari, wasu gaggagaggan ‘yan siyasan da suka iso jihar sun hada da tsohon gwamnan jihar Ogun Mista Segun Osoba da tsohon gwamnan jihar Ekiti Mista Segun Oni da mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Kudancin Nijeriya, Mista Otunba Niyi Adebayo, wanda shi ne gwamnan farko da aka zaba a jihar Ekiti a shekarar 1999.

Sauran sun hada da gwamnonin jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da Ibikunle Amosun na jihar Ogun da kuma gwamnan jihar Kebbir, Alhaji Isa Bagudu, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin yakin nenman zaben gwamnan jihar Ekiti na jam’iyyar APC.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 15 Boko Haram Tare Da Kwato Makamai A Borno

Sojojin dake gudanar da aikin fatattakar ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas sun samu nasara kashe ‘yan kungiyar Boko Haram 15 a jihar Borno.

Sojojin sun fito ne daga ‘7 Brigade, Sector 3’ na dakarun hadin gwiwa sun kuma yi artabu ne da ‘yan ta’addan a garin Arege a yayin da suke aikin sintiri a yankin.

Kayayyakin da aka karbe daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da bindigar harbor jiragen sama guda 1 da bindiga kirar AK 47 guda 5 da da kuma babbar bindiga mai kai farmak daga besa guda 1.

Daraktan watsa labarai na rundunar sojojin Nijeriya, Brigediya Janar Tedas Chukwu, ya sanar da haka a wata takardar sanarwa daya raba wa mane ma labarai, in da ya kara da cewa, soja daya ya ji rauni a artabun da aka yi, yana kuma karbar magani a asibitin sojoji.

Sanarwa ta ci gaba da cewa, “Dakarun ‘7 Brigade, Sector 3’ na hadadiyyar rundunar tsaro sun yi artabu da ‘yan ta’addan Boko Haram a garin Arege, ta jihar  Borno State.

“A artabun da aka yi mun samu nasarar kashe 15 daga ciknsu yayin da wasu suka tsere cikin daji da munanan raunuka..

“Jami’anmu na kokarin ganin an cafko ‘yan Boko Haram din da suka tsere cikin daji, kayayyakin da aka sanu nasarar kamawa a hannunsu sun hada da bindigar harbor jiragen sama guda 1 da bingida kirar AK 47 guda 5 da kuma babbar bindiga mai kai farmaki daga nesa guda 1.

“Daya daga cikin sojojinmu ya samu mummunan rauni, a halin yanzu tana karbar magani a asibitin sojoji.

“Muna amfani da wannan daman din buwatar jama’a su gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani lamarin da basu gane masa ba don a dauki mataki..

 


Advertisement
Click to comment

labarai