Connect with us

LABARAI

Hukumar Kula Da Jami’o’i Ta Kasa, Ta Dauke Takunkumin Yin Karatun Jami’a Daga Nesa

Published

on


Hukumar kula da Jami’o’i ta kasa, NUC, ta bayyana cewa, tana nan tana shirya wani gagarumin shiri wanda zai bayar da daman yin karatun Jami’a daga nesa a Nijeriya, wanda wannan ke nu ni da shirin da hukumar ke yi na dauke takunkumin hana yin karatun Jami’an daga nesa.

Babban sakataren hukumar ta NUC, Abubakar Rasheed, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin, sa’ilin da yake magana wajen wani taron kara wa juna sani na kwanaki biyu, wanda aka shirya wa dukkanin mataimakan shugabannin jami’o’in kasaranan, domin kara kintsa kansu kan kalubalen da ke fuskantar manyan cibiyoyin ilimi na kasarnan.

Ya ce, wasu kwararru ne ke kan aikin samar da shirin, da zaran an kammala, hakan zai baiwa hukumar dama da ta lura da yadda shirin karatu daga nesan zai yiwu a cikin Jami’o’in na kasarnan da zaran an dauke takunkumin.

Mista Rasheed, ya nemi dukkanin manyan Jami’o’in kasarnan da su shirya tarban shirin da zaran an kaddamar da shi domin fadada karatu a manyan cibiyoyin ilimi na kasarnan.

Ya yi nu ni da cewa, yawan masu neman shiga Jami’o’in a kasarnan a duk shekara, in an yi la’akari da cikan da Jami’o’in ke yi, tabbas wannan tsarin na yin karatun Jami’an daga nesa zai taimaka matuka gaya.

Sai dai ya ce, hukumar ba za ta yarda da yin karatun Jami’an daga nesa ba kacokam dinsa, domin kar a bayar da filin yin magudi a wajen karatun na Jami’a.

Shugaban hukumar ya nanata cewa, hukumar tana kan sake fasalin tsarin karatun na Jami’o’i, domin kulawa da irin bukatun kasarnan.

Shugaban ya yi nu ni da cewa, matukar ana son samun ci gaban da ake bukata a karatun na manyan makarantu a kasarnan, ya zama tilas ga Jami’o’in mallakan gwamnatoci da kuma masu zaman kansu da su kasance tare domin samun ci gaba mai ma’ana.

Da yake karfafa yin nazarin tsarin karatun a kai-a kai, Rasheed cewa ya yi, “Tsarin namu kara bunkasa yake yi. Muna da sama da Jami’o’i 164 da dalibai milyan biyu a cikin su, tare da malamai 60,000, a cikin tsarin, wannan ya nu na muna da tsari mai girman gaske, wanda yake da bukatan mu rika duba yanayin shi a kowane lokaci.”

Kan jita-jitar matsayin Jami’o’in na Nijeriya a duniya, Rasheed ya ce, hukumar ba taba bayar da wani matsayi ba ga wata Jami’a, ya kara da cewa, a shekara mai zuwa ne za mu bayar da yadda matsayin Jami’o’in yake bayan mun kammala duba komai.

Ya kuma kalubalanci Jami’o’in da su bullo da sabbin shirye-shirye, inda ya ce, hukumar na su a shirye take da ta hada kai a tare da su domin samar da ci gaba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai