Connect with us

LABARAI

Gwamna Ugwuanyi ya cika alkawarinsa na N5 miliyan ga Super Eagles

Published

on


Gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ya ciki alkawarin da yayi yan wasan Nijeriya na kyautar naira miliyan biyar bisa kokarin da suka a gasar kwallon kafa ta duniya da ake gabatarwa a kasar Rasha.

Ya cika alkawarin da yayi musu a ranar Talata, inda ya gabatar wa da takarda kudi ga tawagar ta hanyar Kwamishinan Matasa da Wasanni jihar, Joseph Udedi. Ugwuanyi ya yaba wa yan wasan Super Eagles ya kuma yi musu fatan nasara a kungiyoyin kwallon kafa da suke bugawa.

Gwamnatin Jihar Enugu ta samar da kayan aikin likita na zamani, kayan horo da kayan aikin horo ga kungiyar Rangers FC don bunkasa aikin su da kula da ‘yan wasan da suka ji rauni.


Advertisement
Click to comment

labarai