Connect with us

LABARAI

An Bukaci Kungiyar FOMWAN Ta Yi Yaki Da Shan Miyagun Kwayoyi

Published

on


Gwamnan Muhammad Abdullahi Abubakar ya bukaci kungiyar mata musulmai ta kasa FOMWAN da su kara himma kan wayar da kan mata da yara domin tabbatar da cewar sun zama al’umma na gari.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya amshi bakwancin Amiran kungiyar ta FOMWAN a gidan gwamnatin jihar, ya kara da cewa gudunmawar da kungiyar mata musulmai ke bayarwa wajen gyarawa gami da kyautata tarbiyyan mata da yara abu wanda ke matukar taimaka wa wajen gina kasa, don haka ne ya bukaci kungiyar da kada ta gaza kan wannan namijin kokarin da suke yi.

Gwamnan ya tabbatar da cewar gwamnatinsa a shirye take ta yi aiki kafada-kafada da kungiyar mata musulmai wajen taimaka wa mata da kananan yara domin su ma su kai ga cimma burinsu na rayuwa.

Gwamna Muhammad Abubakar ya kuma yi alkawarin bayar da dukkanin gudunmawar gwamnatinsa wa kungiyar ta FOMWAN domin samun nasarar shirye-shiryensu musamman ta fuskacin kyautata shugabanci a jihar.

Tun da fari, Amiriyar kungiyar ta FOMWAN ta kasa Hajiya Halima Jibrin ta bayyana wa gwamnan cewar an kirkiro kungiyar ne tun a shekara ta 1985 inda suke kan aiki gaya wajen gyaran rayuwar al’umma musamman mata ya fuskacin yada da’awa, kan lafiya, kare martaban mata da kuma ‘yandin dan adam.

Hadiza ta kuma shaida wa gwamnan cewar kungiyarsu na matukar kokari a matakin jihar Bauchi musamman a bangaren shirye-shiryensu na Da’awa, lafiya da kuma fannin lafiya, daga bisani ta shaida wa gwamnan farin cikinsu a bisa kokarinsa na wanzar da zaman lafiya a jihar.

Amiran ta bayyana cewar kawo yanzu FOMWAN tana da makarantun Firamare, Naziri da Sakandari guda 281, hadi da makarantun Islamiyyoyin mata sama da dubu biyu, asibitoci hudu a fadin kasar nan.

A wani labarin makamancin wannan; matar gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza  MUHAMMAD Abubakar ta bukaci kungiyar mata musulmai ta FOMWAN da su taimaka wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin mata da matasa a fadin kasar nan domin kyautata makomar Nijeriya.

Hadiza Abubakar ta shaida hakan ne a lokacin da ta amshi bakwancin shugabanin kungiyar matasa musulmai ta FOMWAN a ofishinta,  ta bayyana cewar wannan kiran nata ya zama tilas la’akari da yadda mata da matasa suka tsunduma kawukansu kan harkar shaye-shayen kwayoyi da sauran kayyakin maye.

Hadiza wacce ita ce shugaban kungiyar matan gwamnonin Arewa tace idan aka hadu hanu waje guda za a iya kawar da matsalar a cikin al’umma don haka ne ta bayyana cewar mijinta wato gwamnan Bauchi ya kaddamar da wata kwamiti mai karfi kan yaki da shan miyagun kwayoyi a jihar.

Don haka ne ta bukaci kungiyar mata musulmai da ta himmatu wajen fadakar da jama’a ta cikin ta’awarta da sauran aikace-aikacenta domin yaki da wannan matsalar.

Da take bayyana dalilansu na kasancewa a ofishin matar gwamnan jihar Bauchi, Shugaban kungiyar mata musulmai ta kasa Halima Jibrin ta bayyana cewar sun zo jihar ne domin jajanta wa matar gwamnan kan da jama’an jihar Bauchi biyo bayan ibtila’in guguwa da gobara da ta sami jihar.

Don haka ne ta bayyana neman goyan baya da matan gwamnan domin inganta rayuwar mata da yara a fadin jihar Bauchi.


Advertisement
Click to comment

labarai