Connect with us

LABARAI

2019: Mun Shirya Fuskantar Dauri Da Kisa –Secondus

Published

on


Shugaban jam’iyyar PDP ya ce, ‘yan adawa Nijeriya a halin yanzu a shirye suke don fuskantar kamu da musgunawa da ma mutuwa a yayin da zaben shugaban kasa na 2019 ke kara gabatowa.

Ya yi wannan bayanin ne a taron da jam’iyyu 39 suka yi a Abuja inda suka sa hannu a yarjejeniyar don fitar da dan takarar shugabancin kasa kwaya daya a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.

Ya ce, gwamnatin Muhammadu Buhari na tafiyar da mulkin kama karya da danniya a kan ‘yan Nijeriya, ya kuma yi gargadin cewa, babu yadda gwamnatin zata iya kashe dukka ‘yan adawa a kasar nan.

Ya kuma yi tir da wannan hali na shugaba Buhari, ya kuma ce, suna da bayanan shirin da ake yi na kamu da daure ‘yan adawa masu taratsi daga cikinsu kafin zaben gama gari na shekarar 2019.

Ya ce, “A makon daya wuce ne gwamnatin APC ta fito da wani doka “Executive Order” wanda dukkan masu lura da al’amuran dake faruwa a fagen siyasa da kungiyoyin faren hula suka kwatanta dokar da dokan nan na zamanin mulkin soja mai lamba “Decree 2”.

“Muna sane da dalilin da yasa suke aikata wannan a daidai lokacin da ake shirye shiryen zabe, saboda sun san cewa, jama’a sun dawo daga rakiyarsu, suna kuma son su makale a kan mulki ko halin kaka, har da amfani da karfi wajen tusasawa ‘yan adawa.

“Amma ba za a iya mana barazana ba, in har da gwarazanmu na baya sun janye daga gwagwamaya da bamu samu dimokradiyyar da muke alfahari da shi ba a halin yanzu ba.

“Dole mu tashi mu tabbatar da doka da oda, tarihi zai tabbatar da kokarin da muke yi a halin yanzu.

“Jagororinmu basu da tsoho sun kuma hada kansu, ta haka ne suka ceto kasar nan daga mulkin kama karya na shekarun baya.

“Daga ganin abin da muke yi a yau, dukkan alamu na nuna cewa, babu tsoro tare damu, Allah kuma yana tare damu saboda haka dole mu tsaya mu ceto tare da kare mutanenmu.

“A saboda haka ne nike kira garemu da mu tsayu mu kuma kara karfafa juna don ganin mun fatattaki wannan jam’iyyar APC mu kuma kafa gwamnatin hadin kai da za ta kawo wa jama’a sauki a rayuwarsu.”


Advertisement
Click to comment

labarai