Connect with us

LABARAI

‘Yan Sanda Sun Ceto Matar Da Masu Garkuwa Suka Sace A Kebbi

Published

on


A jiya ne rundunar ‘yan sandan jihar kebbi ta samu nasarar ceto matar mai babbar supermarket ta Sha’aban, Alhaji ANas Mai sha’aban  da ke garin Birnin-kebbi da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Lahadin da tagaba a gidan mijin nata da ke a unguwar Badariya a Birnin-kebbi.

Jaridar LEADERSHIP A Yau ta samu bayani ga majiya mai tushe cewa “ Hajiya Sadiya Tsoho JB an sace tane  a ranar Lahadi da ta gabata a gidan mijinta da ke Badariya ta hannun wasu masu garkuwa da mutane inda suka dauke ta zuwa dajin garin Mahuta  da ke karamar hukumar ta Fakai a cikin jihar ta keebi”.

Haka kuma majiyar ta ci gaba da cewa “ masu garkuwa da mutane sun fake a kusa da gidan nasu ne da nufin sace mai gidan ta Alhaji ANas Mai Sha’aban supermarket da ke unguwar Rafin Atiku da ke  cikin garin na Birnin-kebbi a ranar , kan basu gan mijin nata ba sai suka sace matar ta shi bayan dawowar ta daga gaisuwar rasuwar Marigayi Dandare Gaja a ranar Lahadin da aka sace ta”.

Bugu da kari majiyar tace” bayan masu garkuwa da mutane sun sace Hajiya Sadiya Tsoho JB, bayan kwanaki uku sun yi Magana da ‘yan uwan matar ta wayar hannun da maganar su biya Naira Miliya 200 matsayin kudin fansa kafin su saketa”. A cewar majiyar tace” ban sani ba ko sun biya kudi ko basu biya ba kafin a ka ceto taga hannun su”.

A nasu bangare Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar kebbi watau PPRO DSP Mustapha Suleiman yace” rundunar ta ‘yan sandan jihar ta kebbi ta ceto Hajiya Sadiya Tsoho JB a garin Mahuta da ke karamar hukumar mulki a jihar kebbi”.

Ya ci gaba da cewa an sace tane a ranar Lahadin da tagaba ta ne , kwanaki bakwa dasu kashude, kuma an ceto ta a cikin koshin lafiya kuma yanzu haka ta koma cikin iyalan ta domin ci gaba da zaman rayuwa. Ya kuma ce “ rundunar ta ceto tag a hannun masu garkuwa da mutane batare da biyan kudi ba”.

Daga karshe yace” rundunar ta ‘yan sandan na iya kokarin tan a ganin cewa ta cafke masu garkuwa da mutanen da suka sace matar Mai Sha’aban supermarket da ke a Birnin-kebbi”.

 


Advertisement
Click to comment

labarai