Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda 30,000 Aka Jibge Domin Tabbatar Da Tsaro A Zaben Ekiti

Published

on


Babban shugaban ‘yan sandan Nijeriya (IGP) Ibrahim Idris ya bayar da umurnin jibge jami’an ‘yan sanda 30,000 da za su yi aiki domin sanya ido a yayin zaben gwamna a jihar Ekiti a ranar 14 ga Yuli.

A cikin wata kwafin sanarwar da ‘yan sanda suka fitar, dauke da sanya hanun Kakakin ‘yan sandan kasa DCP Jimoh Moshood ya bayyana cewar rundunarsu ta jibge jami’an ne domin wanzar da tsaro da kuma dakile yunkurin ‘yan barandar da ka iya kawo baraka a zaben gwamnan da za a gudanar a wannan jihar ta Ekiti.

Moshood ya shaida cewar aikinsu ne su tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’a walau a lokacin da suke gungune ko kuma a lokacin da suke daidaiku.

Ya bayyana cewar rukunan ‘yan sanda daban-daban ne aka aike da su zuwa wannan jihar domin su dafa wa tsare-tsaren kwamishinan ‘yan sandan jihar domin tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Ya ke cewa; “A dukkanin muhallan kada kuri’u a jihar da yawansu ya kai 2451 a cikin Gundumomi 177 da suke fadin kananan sha shida da suke jihar,” In ji ‘yan sandan,” In ji shi.

Jimoh ya kara da cewa, rukunan jami’ansu da aka jibge sun hada da “Jami’an ‘yan sanda na siniti masi kai-kawo (PMF), sashin aiki akan ‘yan ta’adda (CTU), sashin musamman na masu kare rayuka (SPU), sashin dakile tashin boma-bomai (EOD), kwararrun jami’an ‘yan sanda, gami da sashin da suke aiki da ‘yan sanda da sauran rukunan da aka aike don wanzar da tsaro,” In ji Sanarwar.

Moshood ya shaida cewar ‘yan sandan za su yi aiki ne kafada-kafada da sauran jami’an tsaron da suke kasar nan dukka domin kyautata tsaro da kare lafiyar jama’a a lokacin da aka fara zaben da ma bayan gudanar da zaben.

Ya kara da cewar sun kuma samar da jiragen sintiri guda biyu ‘Helikwafta’, da sauran motocin aiki dukka an tura jihar.

Jami’an ‘yan sandan sun bayar da lambar tuntuba da za a sanar da su kan dukkanin wata barazanar da ka iya tasowa domin su hanzarta daukan matakai a kai lambobin su ne 08062335577, 08035925554, 08081761702.

 


Advertisement
Click to comment

labarai