Connect with us

LABARAI

’Yan Hijirar Borno Fiye Da 35,000 Suka Koma Garuruwan Su -Buratai

Published

on


An bayyana cewa yan gudun hijira sama da 35,000 ne suka koma garuruwan su na asali; wadanda a da suke zaune a sansanoni daban-daban a arewacin jihar Borno, a cikin makonni biyu da suka gabata.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, a sa’ilin da yake gabatar da jawabin rufe bikin tunawa da yan mazan jiya (Nigerian Army Day Celebration), na wannan shekara (2018) wanda ya gudana a jihar Borno.

Tukur Buratai ya bayyana cewa, dawowar yan gudun hijirar zuwa yankunan nasu ya ta’allaka ne samamen da rundunar Lafiya Dole- mai yaki da Boko Haram, ke gudanarwa yanzu haka; wanda aka yiwa lakabi da “Operation Last Hold’’, a arewacin Borno da yankin gabar tafkin Chadi.

Ya bayyana muhimmancin wannan samamen da cewa “domin share fagen sake dawo da yan gudun hijirar yankin; wadanda ke zaune a sansanonin gudun hijira daban-daban a jihar zuwa muhallan su na asali”.

Har wa yau kuma, ya ce burin da suke dashi dangane da wannan aikin sharar karshe ta mayakan Boko Haram, shi ne bai wa manoman da suka koma garuruwan nasu isasshen tsaro a lokacin da suke gudanar da ayyukan su na gona a wannan damina ta bana, da ma a nan gaba.

Da yake yin karin bayani, shugaban rundunar sojan Nijeriya, ya ce a gundumar Gudumbali da ke karamar hukumar Guzamala kadai, akwai fiye da magidanta 25,000- wadanda manoma ne, kuma yan hijira, da suka koma yankin nasu. Yayin a karamar hukumar Kukawa kuma, mutum 10,109 ne suka koma garuruwan su da zama, tare da tsammanin karin wasu adadi nan kusa.

Rahotanni sun nuna cewar, wannan shiri na sharar karshe wa mayakan Boko Haram, an tsara shi ne da nufin kakkabe sauran gyauron da ya rage na mayakan kungiyar daga arewacin Borno da yankin gabar tafkin Chadi, duk a jihar. Wanda zai sahale wa yan gudun hijira da ke zaune a matsugunai daban-daban hanyar dawowa yankunan su, an fara aiwatar dashi tun ranar daya ga watan Mayun wannan shekara. Wanda ake sa ran ya dauki watanni hudu- zai kare a cikin watan Agusta.

Domin ya bai wa jama’ar da aka yanto yankunan nasu kwarin gwiwar komawa muhallin su. Tun ranar 14 ga watan Yuni Tukur Buratai ya kaddamar da samamen “Sharan gona’’- inda aka bai wa jama’a damar yin sassabe da kona sharar gonaki, a shirye-shiryen zuwan aikin gona a daminar bana mai kamawa, cikin wadannan yankuna.

A hannu guda kuma, a ranar daya ga watan Yuli, shugaban rundunar sojojin ya kaddamar da makamancin tsarin a garin  Gudumbali, yayin da kwamandan shirin “operation last hold”, Manjo-Janar Abba Dikko ya bayyana aikin tsaftace garin da suna; share mummunan tunani.

Ta bakin Buratai, sojojin Nijeriya sun ji jiki a kokarin yanto garin Gudumbali daga hannun Boko Haram, wanda ya gudana a shekarar 2015.

Bisa ga wannan ne ma ya sanya rundunar sojan Nijeriya ta gina sakandamin mutum-mutumi a garin domin tunawa da wadannan jami’an tsaro wadanda suka sadaukar da rayuwar su wajen kare kasar su.

 


Advertisement
Click to comment

labarai