Connect with us

LABARAI

Sojoji Sun Ceto Wata Yarinya Daga Maboyar Kungiyar Boko Haram

Published

on


Dakarun sojojin Nijeriya a Borno sun ceto wata yarinya da ‘yan kungiyar Boko Haram suka gudu suka barta yayin da sojojin suka fatattakesu, jami’in watsa labaran rundunar, Birgrdiya Janar Tedas Chukwu ya sanar da haka.

Sanarwa da Chukwu ya watsa ta ci gaba da cewa, sojojin sun kuma kama bindiga kirar AK47 guda 3 da bindigar FN guda daya da kuma rigar da ‘yan kunar bakin wake ke sawa in zasu kai hari guda daya daga ‘yan ta’addan.

Ya kuma ce, an kuma kwato batir guda daya da bam na hannu guda 36 da baturan hada bam guda 9 da wasu kayayyakin da ake hada bama bamai dasu da kuma injinan mika guda 2.

A wata sabuwa kuma, Birgediya Chukwu ya ce, fiye a mutane 1, 843 suka amfana da harar samar da kiwon lafiya da rundunar sojojin Nijeriya suka gudanar a karamar hukumar Bama na jihar Borno, ya ce, samar da kiwon lafiyar na cikin shirye shiryen bikin ranar sojoji na kasa ‘Nigerian Army Day’ da aka gudanar kwanan nan.

 


Advertisement
Click to comment

labarai