Connect with us

LABARAI

Sauya Sheka: Umurnin Saraki Mu Ke Jira –APC Reshen Kwara

Published

on


‘Ya’yan Jam’iyyar APC a Jihar Kwara sun ce, su yanzun umurnin Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Bukola Saraki, suke jira domin su san ko za su fice ne daga Jam’iyyar ta APC.

Shugaban Jam’iyyar na Jihar, Honorabul Balogun-Fulani, ne ya bayyana hakan wajen wani taron manema labarai a Ilorin jiya, ya ce, har kullum biyayyarsu ta na ga Sarakin, duk kuma shawarar da ya yanke ita za su bi. Balogun-Fulani, ya bayyana Jam’iyyar ta APC a matsayin Jam’iyyar da ta fashe, ya yi jimamin yadda hadin kan da ke cikin Jam’iyyar duk ya tarwatse saboda rigingimu da kuma yadda aka yi ta jagwalgwala shari’ar da ake yi wa Sarakin.

Shugaban Jam’iyyar ya ce, tun a makon da ya gabata ne Sanatoci ukun da ke wakiltar Jihar, wadanda duk suna wajen taron na jiya,  suka kira shi, suna neman shi da ya roki Sarakin da ya hanzarta fitar da su daga cikin Jam’iyyar ta APC.

Tun da farko, Balogun-Fulani, ya bayyana farin cikinsa ne kan yadda kotun koli ta wanke tare da sallaman Sarakin kan zargin yin bayanan karya kan kadarorin da ya mallaka, wanda aka kwashe shekaru uku ana ta fafatawa. Ya ce, ai su tuntuni sun san duk sharri ne ake binsa da shi.

“Muna da tabbacin matsin lambar da aka yi ta yi ga jagoran namu, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya samo asali ne daga lokacin da ya nemi ya gwada kwanjinsa, na yin takarar Shugabancin Majalisar ta Dattawa kamar yadda tsarin mulkin kasarnan ya ba shi daman yin hakan, wanda kuma yin hakan bai yi wa wasu shugabannin Jam’iyyar ta APC dadi ba.

 

“Sun yi kokarin bin duk hanyoyin da suke iya bi, da suka ma saba wa shari’a da ma tsarin mulki wajen ganin sun iya tozarta shi, wulakanta shi da kuma a tsige shi daga shugabancin Majalisar ta Dattawa. Don haka, muna ma Allah godiya da wannan nasara da ya ba shi, muna kuma taya jagoranmu murna kan nasarar da ya samu bayan an wahaltu.

“Kamar yadda muka sha fada ne, babu wata Jam’iyyar siyasa da za ta kullawa kanta yaki sannan kuma ta rayu. Tabbas, yanzun dai ta tabbata, hadin kai da yarda da junan da ke cikin jam’iyyar ta APC duk ya tarwatse ya kuma daidaice ya lalace.

“A matsayinmu na Jam’iyya, muna yi ma Sanatocin kasarnan godiya da kuma wakilan majalisar kasa, duk muna kara yi maku godiya, kai hatta ma daukacin ma’aikatan majalisun duk muna gode masu bisa yadda suka tsayu kyam tare da shugaban majalisar ta Dattijai.

“Muna yi ma daukacin ‘yan Nijeriya masu riko da soyayyar dimokuradiyya, wadanda suka aminta da bin dokokin kasa godiya, bisa yadda suka tsayu a tafarkin dimokuradiyya a wannan lokacin da aka yi ta azabtar da masoyan dimokuradiyyan.

“Musamman, muna kara gaisuwan ban girma ga ‘ya’yan Jam’iyyar APC a nan Jihar Kwara da ma Nijeriya bakidaya, wadanda suka yi ta wa Shugaban majalisar ta Dattawa fatan alheri. Da fatan Allah Ya ci gaba da kasancewa a tare da ku.

“A karshe, muna son mu nanata a bayyane, matsayarmu na biyayyarmu kacokam ba kuma tare da wani kaidi ba ga jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki. Ko ta wane hali, mai dadi ko marar dadi duk muna tare da shi,” in ji Balogun-Fulani.


Advertisement
Click to comment

labarai