Connect with us

LABARAI

Sakamakon Garkame Ofishinta, MTN Ta Amince Da Sharadin NLC A Kano

Published

on


Kungiyar ‘yan kwadago ta kasa, NLC reshen Jihar Kano, karkashin shugabancin kwamared Kabiru Ado Minjibir ta bi sahun Kungiyoyin na NLC a matakan Jihohi wajen garkame ofishin kamfanin sadarwa na MTN a Kano.

A Jawabinsa, Kwamared Kabiru Ado magayakin Minjibir ya bayyana cewa babban dalilin bayyanarsu a wannan ofis tun karfe shida na safe shi ne don su rufe ofishin MTN na Kano kamar yadda suka samu umarni daga matakan shugabancin NLC ta kasa.

Umurnin wanda ya biyo bayan sakamakon azabtar da ma’aikatan MTN da kamfanin yake yi ta hanyar hana su shiga kungiyoyin ma’aikata da kuma hana su yin kungiya a kamfanin na MTN. Sai kuma kasancewar ma’aikatan MTN kashi 80 cikin 100 na wucin Gadi ne bana dindindin ba. Ga kuma korafin al’umma akan rashin gamsuwarsu da yadda MTN ta ke wa masu hulda da ita, don haka ne uwar kungiyar kwadago ta umarci ‘ya’yanta da su rufe ofishin MTN tun daga jiya zuwa Laraba domin tilasta wa MTN bin doka da oda ta ka’idojin aiki na kasa da ma na duniya bakidaya.

Babban Jami’in riko na MTN, shiyyar Kano, Abdulhamidu Hassan ya bayyana cewa za su bi wadannan sharudda na kungiyar NLC, wurin ba da dama ga ma’aikatansu su yi kungiya kamar yadda NLC ta bukata. Kuma da ma ma’aikatan su kala biyu ne, wanda suka dauka da kansu da kuma wanda wani kamfani ya kawo musu bisa Yarjejeniya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai