Connect with us

LABARAI

NAFDAC Za Ta Dau Matakin Hana Shigo Da Barasa Mara Rajista

Published

on


Hukumar NAFDAC ta bayyana cewar, zata dauki dukkan matakin daya dace don hana shigo da barasan da basu da ragista cikin kasuwannin kasar nan.

Shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayar da wannan sanarwar a Abuja ranar Lahadi daya gabata.

“Hukumar NAFDAC na kokarin ta takaita shigo da wadannan barasan ta hanyar hana ragista ga kanfanin barasan da suka karya ka’idar da ake a kasa,” inji ta.

Adeyeye ta kara bayyana cewa, wannan bayanin na cikin kudurin data gabatar a taron kasa da kasa karo 41 ‘Coded Alimentarious Commission (CAC)’ da aka gabatar a garin Rome ta kasar Italiya.

Kungiyar ‘Coded Alimentarius Commission (CAC)’ wata hadaka ce ta kasa da kasa mai mambobi 180 an kafa kungiyar ce a karkashin kungiyar ‘Food and Agriculture Organization’ da albarkacin kungiyar majalisar dinkin duniya ta ‘Food and Agriculturr Oganizatio (FAO) da kuma hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya ‘World Health Organisation (WHO)’ da nifin tsaftace harkoki abinci da abin sha a duniya baki daya.

A na nufin kare masu amfani da abinci da abin sha a fadin duniya da kuma tabbatar da daidaito a tsakanin kaashe a harkar kasuwanci haka kuma a kungiyar na kokarin samar da fahitar juna da aiki tare da hukumomin kula da abinci a fadin duniya.

“A halin yanzu a na sayar da barasa a leda a fadin kasar nan wannan kuma wani abu ne dake tsananin hatsari ga yara kanana a nijeriya saboda saukin samu da kudin sayensa.

“Amfani da barasa na kawo tarnaki ga ci gaban kasa, yanan kuma da matukar illa ga lafiya da zamantakewar  mai shan barasar, yana kuma kawo tarnaki a dangantakar dake tsakanin mai shan barasa da abokanansa da ‘yan uwansa da kuma abokanan aikinsa, daga karshe shan barasa na iya lallata zamantakewa da tattalin arzikin jama’a gaba daya.”

Shugaban hukumar The NAFDAC ta kara da cewa, shan barasa na sanadiyyar aukuwar cututtuka fiye da 200 wadanda suke shafan yaruwar iyali nada ‘ya’ya gaba daya.

Daga nan ta kuma ce, saha barasa na sanadiyar aukuwar cututtukan dab a a daukarsu kamar citar kansa,  mashayin giya kuma yana iya aukar da hatsari a kan hanyoyimu, abin dake iya sanadiyyar rasuwar mutane da asarar dukiyoyi.

Farfesa Adeyeye, ta ce, tsarin ragita na ‘Coded Alimentarius’ nada nifin gabatar da kayayyaki ne a kasuwannin duniya da alamomi guda daya domin kare masu amfani da kayayyakin da kuma samar da daidaito a harkar kasuwanci tsakanin kasa da kasa.

“Wadanna aiyyukan sun yi daidai da dokar data kafa hukumar NAFDAC wanda suka hada da karewa da kuma tabbatar da komai na tafiya a cikin tsari a harkokin da suka shafi shigowa da fitarwa da hakowa da sarrfawa da tallatawa da kuma rarrabawa da kuma amfani da abinci da magunguna a fadin tarayyar Nijeriya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai